✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Firaministan Mali Modibo Keïta ya rasu

Modibo Keïta ya rasu a kasar Morocco yana da shekara 78.

Tsohon Firaministan Mali, Modibo Keïta, ya rasu a kasar Morocco inda ake jinyar sa.

Gwamnatin kasar Mali ta ce Mista Modibo Kéita ya rasu yana bayan shafe shekara 78 a ban kasa.

“Mun samu rahoton rasuwar tsohon Firaminista Modibo Kéita a safiyar yau (Asabsar),” inji sashin yada labarai na Ofishin Firaministan Mali.

Tsohon Shugaban Mali da aka hambarar da gwamnatinsa, Ibrahim Boubacar ya nada misata Kéita a mukamin Firaminista a ranar 8 ga Janairu, 2015.

Mista Kéita ne ya maye gurbin Moussa Mara bayan harin da ’yan tawaye suka kai wa sojojin kasar a yankin Kidal a ranar 14 ga watan Mayun sheakar.

Gabanin zamansa Firaminista a mulkin Boubacar Keita, a 2012 gwamantin tsohon Shugaba Alpha Omar Konaré na dana shi firaminista.