✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohon gwamnan Borno Muhammad Goni ya rasu

Tsohon gwamnan jihar Borno, Alhaji Muhammad Goni ya rasu ranar Laraba bayan wata gajeriyar rashin lafiya. Marigayin shi ne farkon gwamnan farar hula na jihar.…

Tsohon gwamnan jihar Borno, Alhaji Muhammad Goni ya rasu ranar Laraba bayan wata gajeriyar rashin lafiya.

Marigayin shi ne farkon gwamnan farar hula na jihar.

Goni tsohon ma’aikacin gwamnati ne kuma shi ne gwamnan jihar Borno daga shekarar 1979 zuwa 1983 a jamhuriya ta biyu.

An haife shi a shekarar 1942 a garin Kareto da ke a karamar hukumar Mobbar a jihar Borno.

Ya yi karatun firamare a birnin Maiduguri daga shekarar 1953 zuwa 1955, ya yi makarantar sakandare ta Borno a shekarar 1956 zuwa 1961 inda ya wuce wata makarantar ta sakandare a Kano a shekarar 1962 zuwa 1963.

Ya kuma yi karatu a sashen koyar da ilimin tsare-tsare a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarar 1964 zuwa 1987 inda ya yi karatun kwarewa a harkokin kasashen waje.