✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon gwamnan Sakkwato Garba Nadama ya rasu

Tsohon gwamnan tsohuwar jihar Sakkwato a jamhuriya ta biyu, Dokta Garba Nadama, ya rasu yana da shekara 82 a duniya. Ya yi  mulkin jihar ne…

Tsohon gwamnan tsohuwar jihar Sakkwato a jamhuriya ta biyu, Dokta Garba Nadama, ya rasu yana da shekara 82 a duniya.

Ya yi  mulkin jihar ne dai a matsayin gwamna daga watan Janairun 1982 zuwa watan Nuwamban 1983 bayan rasuwar gwamnan jihar na farko zabebbe, wato marigayi Alhaji Shehu Kangiwa.

Ya yi karatun digirinsa na uku a fannin tarihi a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya.

Ya rasu ya bar matan aure uku da ‘ya’ya da jikoki.

Iyalan marigayin sun tabatar da rasuwar ga Aminiya.