✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Hadimin Ganduje ya zama dan takarar Gwamnan Kano a PRP

Tsohon kakakin na Ganduje ya samu kuri'a 120 a zaben fidda-gwanin gwamnan PRP.

Tsohon Hadimin Gwamnan Jihar Kano, Salihu Tanko Yakasai, ya samu tikitin takarar gwamna a jam’iyyar PRP a Kano bayan doke abokan hamayyarsa.

Saliu Tanko Yakasai ya samu kuri’a 120, yayin da abokan karawarsa irin su Habibu Na’allah ya samu kuri’a 25, sai Ghali Sule ya samu kuri’a 20.

Shugaban Kwamitin Zaben Fidda-gwanin Gwamnan Jam’iyyar APC, Hakeem Baba-Ahmed ne ya sanar da hakan bayan kammala kirga kuri’un da aka kada guda 173, wanda guda shida dagda ciki suka kasance lalatattu.

Sakamakon zaben fidda-gwanin shugaban kasa a jam’iyyar ya nuna Kanal Gbolubegba Erosimi Mosugu na da kuri’a 3, Dokta Usman Bugaje na da kuri’a 79, Kola Abiola na da kuri’a 77, sai Patience Ndidi mai kuri’a 5.

Salihu Tanko Yakasai, wanda Tsohon Hadimin Gwamnan Jihar Kano a Kafafen Watsa Labarai ne, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar bayan raba gari da Ganduje.

A watan Fabrairun 2021, Ganduje ya sallami Yakasai daga aiki sakamakon suka da kalubalantar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan sha’anin tsaro.

Yasakai, lokacin da yake bayyana ficewarsa daga APC, a watan Maris din 2021, ya ce jam’iyyar ta gaza cika wa ’yan Najeriya alkawuran da ta daukar musu.