Tsohon Hadimin Ganduje zai tsaya takarar Gwamnan Kano | Aminiya

Tsohon Hadimin Ganduje zai tsaya takarar Gwamnan Kano

Ganduje da Dawisu
Ganduje da Dawisu
    Rahima Shehu Dokaji da Seun Adeuyi

Tsohon hadimin gwamnan Jihar Kano na musamman kan yada labarai a kafofin sadarwar zamani, Salihu Tanko Yakasai, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Jihar Kano a zaben 2023 da ke tafe.

Yakasai ya bayyana hakan ne cikin wani sako da ya wallafa ranar Talata a shafinsa na Twitter.

Tsohon hadimin gwamnan wanda aka fi sani da Dawisu ya ce zai ayyana takararsa a hukumance ranar Juma’a mai zuwa.

Wannan na zuwa ne makonni bayan ficewarsa daga jam’iyyar APC, inda ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PRP.

Idan ba a manta ba dai a watan Fabrairun 2021 ne gwamna Ganduje ya sauke shi daga mukaminsa bisa dalilinta na cewa Yakasan na maganganun da ba su kamata ba da kuma sukar shugaban kasa Muhammadu Buhari.