✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Kwamishinan Ganduje ya soki rashin saurin gyaran titin Kano-Abuja

Tsohon Kwamishinan Ayyukan Jihar Kano wanda Ganduje ya cire saboda zargin murnar mutuwar marigayi Abba Kyari, Hon. Mu’azu Magaji ya yi caccaka kan yadda aikin…

Tsohon Kwamishinan Ayyukan Jihar Kano wanda Ganduje ya cire saboda zargin murnar mutuwar marigayi Abba Kyari, Hon. Muazu Magaji ya yi caccaka kan yadda aikin titin AbujaKano ke tafiyar wahainiya.

Hon. Mu’azu Magaji wanda aka fi sani da Dan Sarauniya, ya bayyana takaicin nasa ne ta shafinsa na Facebook.

“Hakika yadda aikin titin Abuja zuwa Kano ke gudana a yanzu abun takaici ne; abin haushi ne a ce ba za a iya kammala aikin titin ba sai a 2025.

“Akwai hanyoyi da dama da za a iya kara saurin aiki ta hanyar inganta tsarin kwangilar, tsara lokaci, samar da wadatattun kayan aiki da wuri, sakin kudin aikin, samar da wadatattun ma’aikata, sannan uwa uba sanya idanu kan yadda aikin ke gudana”, inji Dan Sarauniya.

Idan ba a manta ba, a cikin makon nan ne Ministan Ayyuka da Gidaje Babatunde Fashola, ya shaida wa wani taron masu ruwa da tsaki a Kaduna, cewa, aikin titin ba zai kammalu ba sai a 2025.

“Nan da 2022 za a kammala hanyar Kaduna zuwa Zaria, wanda wannan babban cigaba ne.

“A 2023 za a kammala hanayar Kaduna zuwa Kano, a 2025 kuma za a kammala Abuja zuwa Kano baki dayanta”, inji Fashola.

Tawagar Gwamnatin Tarayyar da ya jagorant ta yi rangadin aikin hanyar ta Kaduna-Kano wadda ta ce ta gamsu da yadda yake tafiya, duk da cewa ’yan Najeriya na korafi tafiyar hawainiyarsa.