✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon lakcaran KADPOLY ya harbi matarsa ya kashe kansa

Ita kuma matar tasa lakcara ce a Jami’ar Jihar Kaduna (KASU).

Ana zargin wani tsohon babban lakcara a Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Kaduna (KADPOLY) Austin Umera ya kashe kansa.

Ana kuma zargin Mista Austin Umera ya harbi matarsa, Dokta Maurin, lakcara a Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) a gidansu da ke Kigo Road a garin Kaduna.

A halin yanzu dsai Dokta Maurin na kwance a Babban Asibitin Sojoji na 44 da ke Kaduna inda ake jinyarta.

Shi kuma mijin nata an kai gawarsa an ajiye a mucuwari a Asibitin Kwararru na Barau Dikko da ke Tudun Wada.

Aminiya ta samun labarin cewa danyen aikin ya faru ne da misalin karfe 10 na dare ranar Laraba.

Babu cikakken bayan game da hakikin abin da auku amma, Kakain Rundunar ’Yan Sandan Jihar, Kaduna, Mohammed Jagile ya tabbatar da faruwar lamarin.