✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohon Mataimakin Gwamnan CBN, Obadiah Mailafia, ya rasu

Obadiah Mailafia ya riga mu gidan gaskiya.

Tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Obadiah Mailafia, ya riga mu gidan gaskiya.

Wani dan uwansa ya tabbatar wa wakilinmu cewa Mailafia ya rasu a Asibitin Kwararru na Gwagwalada, Abuja, bayan rashin lafiya.

Ya bayyana cewa kafin rasuwar mamacin, ya shaida masa cewa yana fama da zazzabin cizon sauro da mura.

Ya shaida mana cewa da farko ya kira lambar Mailafia domin ya yi masa  godiya kan alherin da ya yi masa, amma ba  ta shiga.

Daga baya sai ya kira daya wayar inda marigayin ya shaida masa cewa ya kashe dayar ce saboda ana damun sa a kanta alhali yana bukatar hutu saboda rashin lafiya da yake fama da ita.

Ya ce bayan wayar da suka yi har ya yi  masa addu’ar samun sauki, ranar Lahadi da safe kuma sai aka kira shi ana sanar da shi rasuwar Mailafia.

A cewarsa, kungiyar ci gaba al’ummar kauyensu na daga cikin wadanda suka aika musu da sakon ta’aziyya.

A baya-bayan nan dai marigayi Mailafia ya shiga labarai kan tataburzar da ke tsakaninsa da hukumar tsaro ta DSS kan zargin ta’addanci da ya yi wa gwamnoni.