Tsohon Ministan Najeriya daga jihar Kano ya riga mu gidan gaskiya | Aminiya

Tsohon Ministan Najeriya daga jihar Kano ya riga mu gidan gaskiya

Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje
Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje
    Ishaq Isma'il

Tsohon Ministan Harkokin Gidan Waya a Jamhuriyya ta biyu, Sanata Hamisu Musa, ya riga mu gidan gaskiya bayan ya shafe shekaru 89 a duniya.

Ajali ya katse hanzarin Sanata Hamisu da misalin karfe daya na daren ranar Alhamis a Asibitin Koyarwa na Mallam Aminu Kano, inda ya yi jinya ta takaitaccen zango kamar yadda wani dansa, Ibrahim Musa ya labartawa manema labarai.

Marigayi Hamisu ya yi karatu a Cibiyar Nazarin Harkokin Gudanarwa da ke birnin New York na kasar Amurka.

A shekarar 1979 ne aka zabi Marigayi Hamisu a matsayin Sanata mai wakiltar shiyyar Kano ta Kudu maso Yamma a karkashin inuwar tsohuwar jam’iyyar PRP.

Yayin zamansa a Majalisar Dattawa, ya jagoranci Kwamitin Walwala da Cigaban Al’umma.

Kazalika, ya samu digirin karramawa ta Dakta da kuma lambar girma ta kasa wato Commander of the Order of the Niger (CON).

A sanarwar da iyalansa suka fitar, za a yi jana’izarsa a ranar Alhamis a gidansa da ke Kafin Agur a Karamar Hukumar Madobi ta Jihar Kano.