✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon shugaban Angola Dos Santos ya rasu

Tsohon Shugaban Angola José Eduardo dos Santos ya rasu, sakamakon wata doguwar jinya da ya yi fama da ita tun daga shekarar 2019 zuwa yanzu.…

Tsohon Shugaban Angola José Eduardo dos Santos ya rasu, sakamakon wata doguwar jinya da ya yi fama da ita tun daga shekarar 2019 zuwa yanzu.

Fadar Gwamnatin kasar ta sanar cewa ya rasu ne a safiyar Juma’ar nan.

Sanarwar ta ce ya mutu ne a asibitin Teknon da ke birnin Barcelona na kasar Spain, inda ake jinyarsa sakamakon doguwar jinyar da ya sha fama da ita.

Shugaba Dos Santos, mai shekara 79, ya shafe kusan shekara 40 yana jagorantar kasar, wacce ke da tarin arzikin mai da ma’adinai.

Magajinsa, shugaban Angola mai ci, Joao Lourenco, ya ayyana kwanaki biyar na zaman makoki da za a yi a kasar.

Lourenco ya bayyana Dos Santos a matsayin wani mutum na musamman ga kasar Angola, wanda ya sadaukar mata da kansa tun yana shekarun samartaka.

Marigayi Dos Santos yana daya daga cikin shugabanni mafi dadewa a nahiyyar Afirka, wanda ya sauka daga mulki shekaru biyar da suka gabata.

Ya sha bayyana kansa a matsayin shugaban kasa na bazata, wanda ya karbi ragamar mulki bayan shugaban Angola na farko, Agostinho Neto, ya mutu a aikin tiyatar cutar kansa a shekarar 1979.

An shafe lokaci mai tsawo ana yakin basasa a kasar a zamanin mulkinsa, inda a shekarar 2002 ce Dos Santos ya yi galaba kan bayan an kwashe kusan shekaru 30 ana gwabzawa da ’yan tawayen UNITA – da Amurka ke goyon baya.