✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Shugaban Asibitin Mallam Aminu Kano ya rasu

Tsohon Shugaban Asibitin Koyarwa na Mallam Aminu da ke Kano, Farfesa Abdulhamid Isa Dutse, ya riga mu gidan gaskiya a Yammacin jiya na Litinin bayan…

Tsohon Shugaban Asibitin Koyarwa na Mallam Aminu da ke Kano, Farfesa Abdulhamid Isa Dutse, ya riga mu gidan gaskiya a Yammacin jiya na Litinin bayan ya yi fama da ‘yar gajeriyar rashin lafiya.

Wani makusanci ga iyalan Marigayin ya sanar da cewa za a yi jana’izar sa da misalin karfe 10 na safiyar Talata a masallacin Alfurqan da ke Nasarawa GRA.

Tun bayan kwantar da shi a sashen ba da kula wa ta musamman na babban asibiti, an rika barar addu’o’in al’umma da su nema masa samun waraka a wurin Mai Duka inda bayan ‘yan sa’o’i kadan ya ce ga garinku nan.

An haifi marigayi Farfesa Dutse a watan Dasumban 1960 a Unguwar Gini da ke tantagwaryar birnin Kano, inda ya yi karatunsa a Firamaren Kwalli a shekarar 1966 gabanin ya koma Makarantar Firamare ta Magwan.

A shekarar 1972 ne ya samu gurbin karatu a Makarantar Government College Kano wadda a yanzu ake kiranta da Kwalejin Rumfa (Rumfa College).

Daga nan Farfesa Dutse ya samu gurbin karatun Likitanci a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar, inda ya samu nasarar kammala karantun kwarewa a aikin Likitan Yara a shekarar 1982 a matsayin dalibin da ya fi kowanne hazaka da samun sakamako mafi kyawu cikin sa’o’insa a lokacin.

Gabanin ajali ya katse masa hanzari, ya rike mukamai daban-daban a Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Kano da wasu wuraren na daban.