Tsohon Shugaban BBC Hausa ya rasu | Aminiya

Tsohon Shugaban BBC Hausa ya rasu

Barry Burgess
Barry Burgess
    Sagir Kano Saleh

Allah Ya yi wa tsohon Shugaban Sashen Hausa na BBC, Barry Burgess rasuwa.

Marigayi BBC, Barry Burgess ya rasu Asabar a gidansa da ke birnin Birmingham a Burtaniya yana da shekara 72 a duniya.

Mista Barry Burgess, wanda ya rasu a cikin barcinsa ranar Asabar a Burtaniya, ya ba da gagarumar gudummawa wajen bunkasa harshen Hausa a duniya.

An haife shi ne a 1948 kuma ya fara aiki da BBC ne a shekarar 1974 a matsayin mai hada shiri a Sashen Hausa kafin daga baya ya bar BBC ne a matsayin shugaban sashen a shekarar 1999.