✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon shugaban Burkina Faso ya samu ’yanci bayan daurin talala

An jibge masa jami'an tsaro don tabbatar da tsaron lafiyarsa.

Sojojin Burkina Faso sun saki tsohon shugaban kasar Roch Kabore, wanda ke tsare a hannunsu tun bayan juyin mulkin da suka yi masa a watan Janairun da ya gabata.

Gwamnatin mulkin sojan Burkina Fason ta ce an bai wa Kabore damar komawa gidansa da ke Ougadougou babban birnin kasar a ranar Laraba, inda aka sanya matakan tsaro don “tabbatar da tsaron lafiyarsa”.

A watan da ya gabata, shugabannin Kasashen Yammacin Afirka suka bukaci gwamnatin sojin ta saki tsohon shugaban kasar tare da gaggauta tsayar da lokaci na “mafi karbuwa” na shirya zabe domin komawa ga tsarin mulkin dimokuradiyya, sabanin lokacin da suka tsara na shafe watanni 36 suna rikon kwarya.

Ya zuwa yanzu dai gwamnatin mulkin sojan Burkina Faso na ci gaba da yin watsi da matsin lamba daga kungiyar kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS, kan neman yin murabus daga mulki cikin kasa da shekaru uku, tana mai cewa abin da ta sa gaba shi ne magance matsalar rashin tsaro a fadin kasar.