✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohon shugaban Hukumar Hana Fasa-kwauri, Dikko Inde, ya rasu

Ya rasu yana da shekaru 61 da yammacin ranar Alhamis bayan fama da gajeriyar jinya.

Tsohon shugaban Hukumar Hana Fasa-kwauri ta Najeriya, Dikko Abdullahi Inde ya rasu.

Wata majiya daga iyalan mamacin wacce ta tabbatar da labarin ta ce marigayin ya rasu ne a gidansa dake yankin Jabi a Babban Birnin Tarayya Abuja.

Ya rasu yana da shekaru 61 da yammacin ranar Alhamis bayan fama da gajeriyar jinya.

Majiyar ta ce, “Ya yi fama da matsananciyar rashin lafiya kuma an kai shi wani asibiti dake kusa da gidansa a Jabi, Abuja, kafin daga bisani kuma ya rasu a gida yana da shekaru 61.

“Mutuwarsa wani gagarumin rashi ne, Allah ya gafarta masa,” inji majiyar.

Tsohon shugaban dai ya sha fuskantar tuhuma kan zarge-zargen rashawa daga hukumomin yaki da cin hanci na EFCC da ICPC bisa zarginsa da azurta kansa lokacin da yake jagorantar hukumar, zarge-zargen da ya sha musantawa.

A baya dai an kwace kadarori na biliyoyin Nairori daga hannunsa.

Ya dai shugabanci Hukumar ta Hana Fasa-kwauri ne tsakanin shekarar 2009 da ta 2015.

An haifi marigayi Dikko Inde a ranar 11 ga watan Mayun 1960 a garin Musawa na jihar Katsina, kuma ya fara aiki da Hukumar Hana Fasa-kwaurin ne tun 1988.