✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Shugaban Jami’ar ABU, Farfesa Mahdi, Ya Rasu 

Tsohon Shugaban Jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya (ABU) kuma Shugaban Jami'ar Jihar Gombe na farko, Farfesa Abdullahi Mahdi, ya rasu

Tsohon Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya (ABU) kuma Shugaban Jami’ar Jihar Gombe na farko, Farfesa Abdullahi Mahdi, ya rasu yana da shekaru 77 a daren ranar Juma’a.

Gwamnan Muhammad Inuwa Yahaya na Jihar Gombe, ya aike da sakon ta’aziyar ne a wata takarda mai dauke da sanya hannun Babban Daraktan Yada Labarai na Gidan Gwamnati, Isma’illa Uba Misilli, inda ya ce rasuwar Farfesa Abdullahi Mahdi, ba karamin rashi ba ne ga duniyar ilimi.

A cewar Inuwa Yahaya, ba za a taba mantawa da farfesan ba a duk jami’oin da ya koyar saboda irin yadda ya ajiye tarihi.

Ya ce rasuwar Farfesa Mahdi, ba karamar rashi ba ce, domin ya bar tarihin da bai zai gogu ba, kuma ya bar gibi a bangaren ilimin tarihi, ba a Najeriya kadai ba, a duniya baki daya.

Za a gudanar da Sallar Jana’izar Marigayin a kofar mai martaba Sarkin Gombe da misalin karfe 4 na yamma ranar Asabar.