Tsohon Shugaban Kasa Jonathan ya auna arziki a hatsarin mota a Abuja | Aminiya

Tsohon Shugaban Kasa Jonathan ya auna arziki a hatsarin mota a Abuja

Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan
Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan
    Ishaq Isma’il Musa

Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya auna arziki a wani mummunan hatsari da ya rutsa da ayarin motocinsa a Abuja.

Bayanai sun ce hatsarin wanda ya yi ajalin wasu hadimansa biyu ya auku ne a Yammacin ranar Laraba.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawunsa, Mr Ikechukwu Eze, ya ce jam’ian yan sanda biyu da ke cikin tawagar sun mutu nan take.

Aminiya ta ruwaito cewa hatsarin ya faru ne a hanyarsa ta komawa gida daga filin tashi da saukar jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke babban birnin kasar.

Tuni dai tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya aike da sakon jaje, yana mai yi wa Allah Godiya da ya tseratar da rayuwar Shugaba Jonathan.

Kazalika, ya jajanta wa iyalan wadanda suka riga mu gidan gaskiya a sakamakon hatsarin.