✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Shugaban Kasar Kenya, Mwai Kibaki, ya rasu

Tsohon shugaban kasar ya rasu yana da shekara 90 a duniya.

Tsohon Shugaban Kasar Kenya, Mwai Kibaki, da ya shugabancin kasar tsawon shekaru 10 a wani lokaci da kasar ta yi fama da rigingimun siyasa ya rasu yana da shekaru 90 a duniya.

Shugaban kasar Kenya na yanzu, Uhuru Kenyatta, ne ya sanar da hakan a ranar Juma’a.

Sai dai ba a sanar da musababbin rasuwar ta shi ba, amma ya jima yana jinya a asibiti.

Kazalika, Kenyatta ya bayyana alhininsa tare da bayyana mamacin a matsayin mutum mai hangen nesa tare da sanin abin da ya kamata a fagen tafiyar da mulkin jama’a.

Mwai Kibaki, tsohon farfesa a fanin tattalin arziki, ya samu horo ne a kasar Uganda kafin daga bisani ya je Landan don samun kwarewa a fanin Tattalin Arziki.

Ya na daga cikin mutanen da suka taka muhimiyar rawa a fagen siyasar Kenya tun bayan samun ’yancin kanta a shekarar 1963.

Ya zama Shugaban Kasar Kenya a 2002 tare da daukar alkawarin yakar cin hanci da rashawa, bayan da Shugaba Daniel Arap Moi ya shugabancin Kenya tsawon shekara 20.

Marigayin, dan kabilar Kikuyu ne kuma yana daga cikin mutanen da suka taimaka wa shugaba Uhuru Kenyatta na jadadda manufofin siyasa zuwa shekara ta 2030 a Kenya.