✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Shugaban Laberiya, Charles Taylor, ya maka gwamnatin kasar a Kotun ECOWAS

Ya zargi gwamnatin Laberiya da kin biyan shi hakkokinsa tun shekarar 2003.

Tsohon Shugaban Kasar Laberiya, Charles Taylor, ya maka gwamantin kasar a Kotun ECOWAS kan zargin kin biyan shi hakkokinsa na tsawon shekara 18.

Charles Taylor ya shaida wa Kotun ECOWAS cewa tun bayan saukarsa daga mulki a shekarar 2003, gwamnatin kasar ba ta biyan shi kudadensa na fansho da sauran hakkokinsa a matsayin tsohon shugaba ba, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tsara.

Ya bayyana wa kotun cewa dokar kasar ta 2003 ta tanadi cewa, “Duk shugaban kasar da ya sauka daga mulki, matukar baya wani aikin gwamnati da ake biyan shi albashi, to za a rika biyan shi kudaden fansho da sauran hankoki daidai da rabin na shugaban kasa mai ci.”

A cewarsa, rashin biyan shi hakkokinsa da gwamnatin Laberiya ta yi tauye masa ’yanci ne a matsayin dan Adam, musamman hakkin samun kariyar doka da na samun adalci, tsare masa mutunci, da na mallaka kamar yadda Sashen na 2,3, 4, 7 da ne 14 na yarjejeriyar kare hakkoki ta kasashen Afirkra suka tanada.

Tsohon madugun yakin, wanda kuma shi ne Shugaban Kasar Liberiya na 22, ya kara da ce dokar kasar da ta tanadi biyan shi fansho ita ta tanadi biyan kudaden fansho ga tsoffin shugabanni da mataimakan shugabannin majalisar tarayyar da ta dattijan kasar da manyan alkalai da kuma shugabanni da alkalan Kotun Koli.

Ta kuma tanadi cewa za a tanadar wa tshon shugaban kasa hadimai da sauran abubuwan da kimarsu ba za ta gaza Dalar Amurka 25,000 a duk shekara.

Matarsa kuma, idan tana raye, za a rika biyan ta rabin kudin fanshonsa da sauran hakkokin.

Idan kuma matar tasa rasu, za a raba wa ’ya’yansu masu kasa da shekara 18 abin da ya kamata a rika biyan matarsa.