✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayan Sallar Juma’a za a yi jana’izar Tsohon Shugaban ’Yan Sanda Gambo Jimeta

Za a yi jana'izarsa bayan sallar Juma'a a Babban Masallacin Kasa, Abuja

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana kaduwarsa da rasuwar tsohon Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Alhaji Mohammed Gambo Jimeta.

Da yake tabbatar da rasuwar Alhaji Gambo Jimeta a Abuja bayan fama da rashin lafiya, kanin mamacin mai suna Abdulrahman Adamu, za a yi jana’izar tsohon Shugaban ‘Yan Sandan na bayan Sallar Juma’a a Babban Masallacin Kasa da ke Abuja.

Buhari yayin ta’aziyyar rasuwar Gambo Jimeta wanda ya ce mutum ne da ya yi rayuwa abar koyi, ya kuma hidimta wa Najeriya  bakin kokarinsa.

“Jarumi mutum ne mai basira kuma dattijon arziki,” inji Buhari yayin da yake  ta’aziyyar mamacin wanda a lokacin rayuwarsa ya jagoranci tawagar ’yan sanda masu binciken kwakwaf.

An haifi Alhaji Gambo Jimeta ne a ranar 15 ga Afrilu, 1937, a Jimeta ya kuma zama Shugaban ’Yan Sandan Najeriya a 1986 inda ya gaji Etim Inyang, shi kuma Aliyu Attah ya gayyace shi a 1990.

Mamacin ya kasance Mashawarci kan Harkokin Tsaron Kasa a gwamnatin soja ta tsohon Shugaban Kasa, Ibrahim Babangida.

Da yake jajantawa, Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na Jihar Adamawa ya ce rasuwar mamacin babban rashi ne ga Jihar Adamawa.

Fintiri ta bakin kakakinsa,  Humwashi Wonisikou, ya ce “Ina jimamin rasuwar hazikin dan sandan da kwarewarsa ta kai shi ga zama Shugaban ‘Yan Sanda.”

Ya ce Jihar Adamawa ba za ta gushe ba tana alfahari da mamacin wanda ya taka gagaruwar ruwa wurin daga martabar Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya.

“Ya yi aiki cikin mutunci da tsare gaskiya kuma yana daga wadanda suka gudanar da wasu manayn bincike-bincike a kasar nana,” inji gwamnan.