✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohuwar matar Jeff Bezos za ta raba $2.7bn kyauta

Tana rabar da wani kaso na kudin da ta samu yayin rabuwar aurensu.

MacKenzie Scott, daya daga cikin mata attajirai mafi kudi a duniya, ta bayyana shirinta na raba kudin da ya kai Dala biliyan biyu da miliyan 700 kyauta ga bangaren samar da ilimi da kula da al’umma da kuma kungiyoyi masu zaman kansu.

MacKenzie wadda ita ce tsohuwar matar Jeff Bezos, attajirin da alkaluma a yanzu syun tabbatar da shi ne mutumin da ya fi kowa kudi a duniya, ta bayyana shirin fitar da wani kaso daga cikin kudin da ta samu yayin rabuwarsu da tsohon mijin nata.

Sashen Hausa na Rediyon Faransa RFI ya ruwaito MacKenzie tana cewa, kungiyoyin da za su amfana da kudaden da za ta rabar sun tasarma 286.

An yi kiyasin cewa MacKenzie ta mallaki dukiyar da ta kai Dala biliyan 59, inda wannan sanarwar ita ce makamanciyarta ta uku da ta gabatar bayan irin wannan taimako na kudi da ya kai Dala biliyan 6 da ta bayar ga daruruwan kungiyoyi da makarantu a fadin Amurka.

Sai dai attajirar ta ki amincewa da bukatar kafa Gidauniyar da za ta rika gudanar mata da irin wadannan ayyuka, inda ta dogara da masu bata shawara wajen gano kungiyoyi da hukumomin da ke bukatar taimako tana kai musu dauki.

A cewarta, ita da masu bata shawara na kokarin ba da wani kaso na dukiyar da ta mallaka domin samar da sauyi da zummar ganin dukiyar bata takaita ga wasu ’yan tsirarun mutane ba.

Attajirar tace babu wani sharadi da za a gindaya wa kungiyoyi ko makarantu ko al’ummar da zasu amfana da gidauniyar wajen gudanar da harkokin su.