✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohuwar Ministar Ilimi za ta dauki nauyin karatun Gwarzuwar Hikayata

Tsohuwar Karamar Ministar Ilimi, Hajiya Aishatu Jibril Dukku, ta sha alwashin daukar nauyin karatun Surayya Zakari Yahaya, daya daga cikin mata uku da suka lashe…

Tsohuwar Karamar Ministar Ilimi, Hajiya Aishatu Jibril Dukku, ta sha alwashin daukar nauyin karatun Surayya Zakari Yahaya, daya daga cikin mata uku da suka lashe gasar gajerun kagaggun labarai ta BBC Hausa wato Hikayata a bana.

A yayin bikin karramar matan uku da suka yi zarra a gasar Hikayata ta 2020 da aka gudanar a ranar Juma’a, Hajiya Aisha wacce take wakiltar mazabar Dukku da Nafada na jihar Gombe a  Majalisar Wakilai, ta sanar da cewa za ta dauki nauyin karatun Surayya Zakari, wadda ta zo ta biyu a gasar.

Shi ma tsohon Shugaban Hukumar Alhazai ta Kasa, Barista Abdullahi Mukhtar, ya sha alwashin bai wa matashiyar wani karin tallafin karatu doriya a kan na tsohuwar Ministar.

Surayya Zakari mai shekaru 25, ta samu wannan tagomashi ne kasancewarta maraya sakamakon rasuwar mahaifinta, lamarin da ya sa ta gaza ci gaba da karatu tun bayan kammala matakin sakandire.

Matashiyar dai ta zo ta biyu a gasar Hikayata ta bana a sakamakon kagaggen labarin da rubuta mai taken “Numfashin Siyasata”.

Labarin “Numfashin Siyasata” labara ne da ya faru a kan wata matashiya wadda ta nemi shiga harkar siyasa da zummar share hawayen al’ummar kauyensu na rashin ci gaba da ya addabe su.

Sai dai kuma al’ummar da ta nemi kawo wa sauki suka juya mata baya, kawai saboda kasancewarta mace.

Saboda jajircewarta wajen neman kawo wa al’ummarta ci gaba ya sa aka hallaka mahaifinta – ita ma an yi yunkurin kashe ta amma ta tsallake rijiya da baya.

A dalilin wannan kagaggen labari da ya haska Surayya a idon duniya har ta kai ga zama daya daga cikin gwarazan matan da suka lashe gasar Hikayata a bana, ya sanya bakin suka ga dacewar su ba ta tallafin karatu saboda irin hazakar da ta nuna.

Aminiya ta ruwaito cewa, wata matashiya ‘yar jihar Sakkwato, Maryam Umar ce gwarzuwar gasar gajerun kagaggun labarai ta mata zalla wato Hikayata a bana.

Labarin “Rai da Cuta” wanda Maryam Umar mai shekara 20 ta rubuta shi ne ya zama zakara a gasar ta shekara-shekara.

Labarin na uku kuma shi ne wanda wata matashiya ‘yar jihar Kano Rufaida Umar Ibrahim ta rubuta mai suna “Farar Kafa”.

Bayan tantance fiye da kagaggun labarai 400 da mata daban-daban suka rubuta, alkalan na BBC Hausa sun fitar da uku da suka yi wa sauran fintinkau.

A tattaunawar da Aminiya ta yi da gwarazan matan uku da suka yi zarra a gasar Hikiyata ta bana, sun bayyana farin cikinsu matuka a yayin da kowace daya daga cikinsu ta ambaci cewa burinta na isar da sako da kuma haskakawarta a idon al’umma sun cika.