✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohuwar sarauniyar kyau ta Amurka ta kashe kanta bayan fadowa daga bene mai hawa 30

Ta kashe kan nata ne ta hanyar fadowa daga gini mai hawa 30.

Matashiyar nan da ta lashe kambun sarauniyar kyau ta kasar Amurka a shekarar 2019, Cheslie Kryst, ta hallaka kanta ta hanyar fadowa daga wani dogon bene mai hawa 30 a birnin New York.

Ta mutu ne tana da shekara 30 a duniya.

Iyalanta ne suka tabbatar da mutuwar tsohuwar sarauniyar a wata sanarwa, inda suka bayyana ta a matsayin wata babbar inuwa a wajensu.

An dai gano gawarta ne a gefen hanyar ginin Orion Condominium da misalin karfe 7:00 na safe.

Marigayiyar dai tana zaune ne a hawa na tara na ginin, kamar yadda kafar yada labarai ta New York Post ta rawaito.

Ko da yake iyalanta ba su yi bayanin musabbabin mutuwarta ba, amma majiyoyi daga sashen ’yan sanda na birnin New York sun cw ta mutu ne sanadiyyar kashe kanta.

Kazalika, kafin rasuwar, ta rubuta wata takarda mai kunshe da wasiyya, inda ta ce ta bayar da dukkan abin da ta mallaka ga mahaifiyarta.

A wata tattaunawa ta wayar salula da jaridar New York Daily News, kaka ga marigayiyar, Gary Fimpkins, ya ce jikar tasa tana da matukar kirki ga yawan fara’a.

“Tana da kirki sosai tare da son taimakon jama’a, samun irinta abu ne mai matukar wahala. Abin takaici ne matuka a ce ’yan sa’o’i da suka wuce tana raye, amma yanzu kuma ta rasu, gaskiya wannan babban rashi ne a wajenmu,” inji shi.