✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsoron Tsigewa: Buni Ya Bai wa ’Yan Majalisar Yobe Tikitin Zarcewa

Mutum 18 cikin mambobin majalisar dokokin jihar Yobe 24 na barazanar tsige Gwamna Mai Mala Buni kan yunkurin maye gurbinsu da wasu

Barazanar tsige Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni da wasu mambobin Majalisar Dokokin jihar su 18 cikin 24 suka yi kan jita-jitar cewar shida daga cikinsu ne kawai za a bari su sake komawa kurensu ya sa gwamnan mayar da takobinsa cikin kube.

Wata majiya mai tushe daga Majalisar ta shaida wa Aminiya cewa, ’yan majalisar 18 ne suka fusata da gwamnan, inda aka ce ya zabo mambobi shida da ya ji dadi sosai tare da ba da fom din tsayawa takara a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC na majalisar dokokin jihar.

Majiyarmu ta bayyana cewa, sauran 18 ne suka hallara a zauren Majalisar suna barazanar tsige shi sakamakon wannan Yunkurin na gwamna.

“Sauran mambobi 18 sun shiga zaman gaggawa inda suka gayyaci shugaban jam’iyyar na jihar tare da nuna mishi wasu muhimman takardu, suka shaida mishi cewa za su tsige gwamnan bisa takardun da suke da su tun da ya ki ba su tikitin kai-tsaye.

Majiyar ta kara da cewa, “Ganin wadannan takardun ne sai shugaban jam’iyyar, Alhaji Muhammadu Gadaka ya roki ’yan majalisar da kada su tsige gwamnan, amma su ba shi lokaci ya gana da gwamnan sai suka  yi mishi bayani, idan har Gwamnan ya ci gaba da rike matsayinsa, za su iya ci gaba da aiwatar da barazanarsu.

“Bayan shugaban jam’iyyar ya tafi, sai suka jira sannan ya dawo ya zo da fom ashirin da hudu ya raba wa ’yan majalisar 24 don janye matsayinsu.”

Idan dai za a iya tunawa, magoya bayan jam’iyyar APC daga mazabu 24 na jihar sun roki gwamnan da ya bar dimokuradiyya ta yi aiki, kada ya goyi bayan wasu ’yan majalisar da suka zarce a majalisar dokokin jihar.

Sun kuma roke shi da ya ba da damar a daidaita da wasu, lamarin da aka ce ya samar da matsalolin.

An ce wasu daga cikin ’ya’yan majalisar tun 1999 ba su kawo wani ci gaba a mazabarsu ba, inda suka sanar da jama’arsu da su roki gwamnan ya tabbatar da sauyi ta hanyar ba da damarmakin dimokuradiyya a Jihar Yobe.

Da wannan sabon al’amari, wasu magoya bayan gwamnatin APC a jihar sun ce suna fargabar ’yan adawa na iya kwace jihar idan jam’iyyar ta ba da kwarin guiwar wuce gona da iri a majalisar ba.

Wakilinmu ya yi kokarin tattaunawa da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Yobe, Ahmed Lawal Mirwa da Shugaban Jam’iyyar, Alhaji Mohammed Gadaka kan wannan lamarin amma duk kokarin ya ci tura saboda ba a iya samun wayoyinsu ba.