✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tukin gangancin babbar mota ya kashe wani lauya

Wata babbar mota ya take wani lauya da dan acaban da ya dauko shi a Karamar Hukumar Keffi ta Jihar Nasarawa. Shaidu sun bayyana wa…

Wata babbar mota ya take wani lauya da dan acaban da ya dauko shi a Karamar Hukumar Keffi ta Jihar Nasarawa.

Shaidu sun bayyana wa wakilinmu cewa tukin gangancin direban motan ya yi ne ya yi sanadiyyar kashe mutanen biyu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Nasarawa Rahman Nansel ya tabbatar da faruwar lamarin, wanda ya ritsa da lauyan mai suna Barisa Chiadikoli I. Ezike.

“‘Yan sanda sun tsare direban motar saboda tukin ganganci a Unguwar Lambu a garin Keffi”.

“Lamarin ya faru ne a ranar Asabar, bayan wani direban DAF ya yi tukin ganganci, ya kade wani dan acaba da fasinjan da ya dauko.

“Bayan sun samu munanan raunuka ‘yan sanda sun kai su Babban Asibitin Tarayya da ke Keffi inda wani likita ya tabbatar da rasuwarsu.

“Yanzu wanda ake zargi yana tsare ana gudanar da bincike a kansa”, inji shi.