✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tun a watannin baya ya kamata a tsige Buhari —Shehu Sani

Sai dai ya nuna kokwanto kan samun nasarar tsigwar

Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya ce tun a watannin baya ya kamata a ce an tsige Muhammadu Buhari daga Shugabancin Najeriya saboda matsalar tsaro.

A ranar Laraba ce dai Sanatocin jam’iyyar adawa ta PDP a Majalisar Dattijai suka yi barazanar tsige Buharin kan yadda matsalar tsaro ke dada ta’azzara, matukar bai magance ta ba nan da mako shida.

Sai dai da yake tsokaci a kan batun yayin wata tattaunawarsa da gidan talabijin na Arise ranar Alhamis, Shehu Sani ya ce Sanatocin sun fusata ne saboda matsalar ta fara shiga Babban Birnin Tarayya Abuja.

Ya ce, “Na san ’yan majalisa, musamman ma Sanatoci sun damu da lamarin matsalar tsaro a Najeriya, saboda zai yi wahala yanzu rana ta wuce ba a kashe ko an yi garkuwa da wani ba, kuma hakan na ci gaba da faruwa musamman a jihohin Arewa maso Yamma.

“Yanzu da yadda wadannan ’yan ta’addan suka fara kai hare-hare yankin Abuja, dole ta sa ’yan majalisa sun tashi tsaye. A nan kuma na ga yunkurin da ’yan majalisa na jam’iyyar adawa suka yi.

“Shugaban Majalisar Dattawa wanda dan jam’iyya mai mulki ne yanzu ya shiga tsaka mai wuya; dole ko dai yanzu ya bi bukatar mutane ko kuma ya bi ta gwamnati da jam’iyyarsa.

“Kuma daga abin da na fahimta, Sanatocin jam’iyya mai mulki suna tare da gwamnati. Sannan ’yan jam’iyyar adawa su ma sun fitar da nasu matsayin a kai. Amma wannan matakin nasu ma ya zo a makare, tun a watannin baya ya kamata a ce sun fara yunkurin yin hakan,” inji Shehu Sani.

Sai dai tsohon Sanatan ya nuna shakku kan samun nasarar matakin, inda ya ce Sanatocin jam’iyya mai mulki ba za su goyi bayanshi ba.