✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tun ba a je ko’ina ba, an fara takaddama kan rijiyar mai tsakanin Bauchi da Gombe

Lauyan ya ce wajen mallakin Gombe ne ba Bauchi ba

Wani lauya mai zaman kansa a jihar Gombe, Abdullahi Muhammad Tamatuwa, ya yi barazanar maka masu ruwa da tsaki a kotu muddin aka mallaka wa jihar Bauchi wajen da za a fara tono mai na Kolmani tsakanin iyakar jihohin biyu.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaban Kasa Muhammad Buhari ke kan hanyarsa ta zuwa kauyen na Kolmani inda za a kaddamar da aikin fara hakar man ranar Talata.

Lauyan, dan asalin Karamar Hukumar Akko da ke jihar Gombe ya ce inda ake aikin hakar fetur na Kolmani a jiharsu yake, ba a Bauchi ba.

Ya ce tsofaffin Gwamnonin jihar Gombe da ’yan majalisa ba su damu da yankin na Kolamani ba dan ko ziyartar wajen ba sa yi da hakan yake nuna kamar hadin baki ne na mallaka wa jihar Bauchi wajen.

Abdullahi Tamatuwa ya kara da cewa manya da masu fada aji na jihar Bauchi su ne ke yawan halartar wajen saboda ikirarin da suke yi na cewa a jiharsu yake, bayan ba haka ba ne.

A cewarsa, shekara da shekaru duk zaben da ake yi a wajen runfunar zabensu na Gombe ne, me ya sa yanzu da arziki ya zo za a mayar da shi jihar Bauchi.

“Rijiyoyi biyar da aka samu a wajen guda hudu duk a Gombe suke daya suke cewa ta su ce ta Bauchi kuma nan ma da aka duba ba Bauchi ba ce, Gombe ce domin tazarar iyakar da rijiyar take da shi da iyakar Bauchi kilimota 2.50 ne,” inji lauyan.

Ya kara da cewa wajen gundumar Tai ne kuma Hukumar Shata Kan Iyaka ta Najeriya ta taba tabbatar da wajen a matsayin jihar Gombe.

Ya ce akwai shaidar kashin makera da aka sa a kan iyakar tun lokacin iyaye da kakanni da ya nuna cewa Kolmani Gombe ce, domin Kolmanin sunan wani kwari ne a yankin.

Daga nan sai ya ce muddin gwamnatin Gombe ba ta shiga lamarin ba, za su kai kotu domin ba za su zuba ido suna gani a zalunci jiharsu ba.