Tun da nake ban taba faduwa zabe ba — Tinubu | Aminiya

Tun da nake ban taba faduwa zabe ba — Tinubu

Bola Ahmed Tinubu
Bola Ahmed Tinubu
    Sani Ibrahim Paki

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023 mai zuwa, Bola Ahmed Tinubu, ya bigi kirjin cewa tun da yake bai taba faduwa zabe ba.

Ya bayyana hakan ne yayin wani gangamin jam’iyyar da aka gudanar a Jihar Ekiti ranar Talata.

An yi gangamin ne don nuna goyon baya ga dan takarar Gwamnan Jihar a zaben da za a gudanar a Jihar, Biodun Oyebanji.

Za a yi zaben Gwamnan Jihar ne ranar Asabar, 18 ga watan Yunin 2022.

A cewar Tinubu, “Ban taba faduwa zabe ba a baya. Duk wanda bai yi zabe ba, ba zai sami kudi ba.”

Dan takarar ya kuma bayyana babbar jam’iyyar adawa ta PDP da cewa jam’iyyar bunkasa talauci ce.

Daga nan sai ya roki mutanen Jihar ta Ekiti da su zabi dan takarar jam’iyyar a zaben mai zuwa.