✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tun daga 1999 ba gwamnatin da ta kai tamu kokari —Buhari

Masu sukar gwamnatin nan ba su ga irin ci gaban da aka samu ba.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewar tun daga shekarar 1999 kawo yanzu, babu gwamnatin da ta yi kokarin da gwamnatinsa ta yi wajen samar da ababen more rayuwa da ci gaban kasa.

Buhari ya bayyana haka ne yayin da ya ke jawabin cikar Najeriya shekara 61 da samun ‘yancin kai a ranar Juma’a.

A yayin jawabinsa, Buhari ya ce abun takaici yadda wasu ke sukar gwamnatinsa ba tare da ganin irin ci gaban da ta samar ba.

“Mun yi nasarar cimma abubuwa da dama cikin shekaru shida; wanda suka hada da abubuwan more rayuwa, daga martabar Najeriya da samar da daidaito a Afirka da sauran kasashen duniya.

“Amma masu suka da kalubalantar gwamnatin nan ba su ga irin ci gaban da aka samu ba, tun bayan zuwan wannan gwamnatin mun mun dakile matsaloli da dama.

“Babu wata gwamnati tun daga 1999 da ta yi abin da muka yi cikin shekaru shida, wajen dawo da Najeriya daidai.

“Za mu ci gaba da bautawa kasar nan; ku saurara sannan mu kare dimokuradiyya da kasarmu.”

Buhari ya ce da yawa daga cikin ‘yan Najeriya na murnar ranar 1 ga watan Oktoba duk da irin kalubalen da kasar ke fama da shi.

Tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo ne shugaba na farko da ya mulki kasar bayan an koma tsarin mulki na dimokuradiyya a shekarar 1999, inda bayan saukarsa ragamar jagorancin kasar ta koma hannun marigayi a Umaru Musa Yar’adua a 2007.

Sai dai wa’adin Yar’adua a karagar mulki bai dauki lokaci ba sakamakon rashin lafiya da ya sha fama da ita wadda a karshe ta yi ajalinsa.

Daga nan ne mulki ya koma hannun tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan wanda ya yi zaman mataimakin Yar’adua a lokacin, inda ya kama akalar jagoranci a 2010 sannan ya mika wa Buhari bayan nasararsa a babban zabe na 2015.