Daily Trust Aminiya - Tun ina da shekara 12 na fara waka – Magajiya Dambatta

Tun ina da shekara 12 na fara waka – Magajiya Dambatta

Magajiya Dambatta mawakiya ce da ke waka tare da kidan kalangu ita ce kuma ta yi wata wakar A sa yara makaraanta 1973 wacce ta yi tasiri matuka akan iyayen yara inda aka samu dalibai da aka sanya a makaranta a wancan lokaci da suka kai 3000 wanda kafin nan ba a samun yara da ake sanyawa makaranta da suka kai 500.

A yanzu haka wannan mawakiya ta makance har ma tana yawon bara.

Fitaccen dan jarida Malam Jafar Jafar ne ya binciko ta, inda bayan ya kaddamar da neman tallafin kudi domin taimakonta aka tara sama da Naira miliyan biyar domin samar mata da gida, da kula da lafiyarta da ci gaba da kula da ita.  Aminiya ta yi takanas ta Kano zuwa wajen tsohuwar mawakiyar wacce ke zaune a Karamar Makoda, inda ta tattauna da ita a kan yadda rayuwa ta kasance da ita bayan kasancewar tauraruwa.

Za mu so sanin tarihin rayuwarki

Sunana na gaskiya Halima Malam Lasan, amma an fi kirana da Magajiya Dambata. An haife ni shekara 84 da suka wuce. Na yi karatun addini daidai gwargwado. A yanzu haka ina da ’ya’yana biyu dukkaninsu maza ina kuma da jikoki 10 da ’ya’yan jikoki 24.

Yaya aka yi kika fara waka?

Tun ina da shekara 12 da haihuwa na fara waka. Ina zuwa wasa wurare daban-dabn ba ma a cikin garinmu kadai ba, har ma da gefen garinmu da suka hada da Sharon Dunawa da Sharon Gulbi. A wancan lokacin idan na je fili idan ba ni na yi waka ba to taron ba ya dadi. Idan na je wuri ba zan yi waka ba to zan kwace makadin na gudu.

Yaushe kika yi aure?

Ina yin wakar kuma sai aka yi min aure da wani mutum, mai suna Yusuf Rabo, sai kuma daga baya, bayan mun rabu na sake auren wani Malam Garba. Amma a wancan lokacin na daina waka sai daga baya na koma na ci gaba da wakata har ma ta zame min babbar sana’a domin babu abin da ban yi da kudin waka ba.

Wadannen wakoki za ki iya tunawa?

Akwai wakar Soriyal da Wakar Taron Gidan Rediyon Kaduna da Wakar A kama aikin gona da Wakar A sa yara makaranta da Wakar Jihar Jigawa da sauransu. Ba zan iya tunawa ba shekarun da yawa.

Yaya aka yi kika yi wakar Soriyal?

Lokacin ina kan hanyata ta dawowa daga Minna inda Makaman Nupe ya gayyace mu biki sai aka fada min cewa za a yi wasa na bikin cikar gidan Rediyon Kaduna shekara 37. Da muka je dukkanin mawaka sun taru su Alhaji Mamman Shata Katsina da sauransu, sai aka nemi na yi waka, nan ne na hau na yi wakar nan tawa ta soriyal wacce kuma daga baya ta shahara.

Yaya aka yi kika makance?

Yau kimanin shekara 11 ke nan da na makance gaba daya amma dama tun ina da shekara biyu da aure idona daya ya sami hakiya. A lokacin ina Fagge har aiki an taba yi min amma idon bai samu ba. Daga baya sai kuma dayan idon shi ma ya kamu da ciwo.

Karin Labarai