✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tuna Baya: Dalilin da muka yi hannun riga da Zakzaky — Abubakar Jibril

Har yanzu ban yanke kauna da hada kan malamai ba.

Sheikh Abubakar Jibril, shi ne Babban Limamin Masallacin Juma’a na Farfaru da ke cikin birnin Sakkwato.

Sanannen malami ne a Najeriya da wasu kasashen Musulmi, kasancewarsa malami mai da’awa da gwargwaya a sama da shekarra 60 da suka wuce.

Aminiya ta tattauna da shi a kan rayuwarsa da harkokin da’awa a Najeriya da sauransu, inda ya bayyana dalilin da tafiyarsu ta watse da Zakzaky:

Aminiya: Malam za mu so sanin tarihin rayuwarka?

Sheikh Jibril: Bismillahir rahamanir rahim. Sunana Abubakar Jibril, Limamin Farfaru. A yanzu ina da shekara 78 da haihuwa.

Na samu na yi karatu a kasar Sudan da Nijeriya. Malaman da nake iya tunawa da na yi karatu a wurinsu a Sudan akwai Sheikh Dokta Khalil Adam da Sheikh Abdullahi Malle.

Bayan na dawo Nijeriya na yi karatu a wurin Malam Umar Diddiba, na yi karatu a Cibiyar Ilmi da na shekara hudu, inda malaman da suka karantar da mu suna da yawa, akwai Malam Shehu Na Liman da Alkali Yahaya Nawawi da Malam Haliru Gidadawa da Malam Abubakar Takatuku da Malam Boyi Wamakko, su dai na iya tunawa.

Yaya shugabbani suka dauki malaman addini?

Tabbas akwai bambanci kan yadda suka dauki malamai, shugabannin baya suna mutunta masu addini kwarai ba kadan ba.

Suna ganin masu addini abokan tafiya ne musamman ta hanyar girmama su da kokarin tafiya tare da su da magoya bayansu.

Alakarsu mai kyau ce ga kuma yi masu kyauta da hidimomi. A yankin Sakkwato har zuwa lokacin (Gwamna Sani) Yarima abin bai tabarbare ba, sau biyu yana saya wa malamai mota sabuwa cikin ledarsu.

Haka Mamuda Shinkafi da ya zo, a Sakkwato Bafarawa ya yi tasa hidima, bayansa Sanata Aliyu Wamakko ma ya yi irin tasa, ba wanda ya taka wa wannan tafiyar birki kamar (Gwamna) Aminu Waziri Tambuwal, ya nuna shi ba ya bukatar gudunmawar malamai a tafiyarsa, ga abin da ya bayyana ba ruwansa da gina malamai da masallatai.

Ni ba shakka ban da wurin sukar Gwamna Tambuwal ga abin da ya shafi taimakawa ni yana aiko min sadakoki a Azumi da Sallah, amma tabbas malamai suna kuka da shi ga abin da ya shafi taimako.

Don an yi min sai na ce komai ya yi daidai, bayan na san korafin da malamai suke yi, ba a tallafa masu ba? An samu ci baya gaskiya a wannan gwamnati.

Wadanne matsaloli ne malaman yanzu suke da su wadanda babu su a baya?

Malamai kamar yadda nake da labari suna cikin matsaloli irin na rayuwa.

A baya Gwamantin Sanata Wamakko ta yi tsari na bai wa malaman zaure da limamai da ladanai alawus duk wata, a yanzu ana ba su sai dai akan samu tangarda a wasu lokuta game da biyan.

Hukumar Zakka da Wakafi da Gwamnatin Alu ta kawo ita ce ke dan wani motsi a jihar, shugabanninta ba su da wani korafi a kan kudin tafiyar da aikinsu, komai yana tafiya daidai a wajensu, nan kadai ne mabukata suke samun tallafi.

Ni shaida ne kan haka, ma’aikatar kawai ce ta rage a jihar da take motsi, a gefen gwamnati.

Wani malami ya yi tsammanin a tallafa masa ko a gina masallaci, ya sani wannan ba ya cikin tsarin Gwamna Aminu, ni yana kyautata min hakan ba dalili ba ne na in fadi karya a matsayina, ko don shekarruna da sana’ata na wuce in yi karya.

Ko arne ya yi shekaruna ba ya karya, ba zan zo in ce yana taimakon malamai ba, wanda ba haka ba ne, duk ni’imar da ake bukata Allah Ya yi min ba yunwa da kishirwa a gidana, da zarar mutum ya yi karya ya gama yawo.

A baya malamai kukan hada kai ku fuskanci lamura. A yanzu kana ganin malamai na da hadin kai a tunkarar lamura?

Ina sa ran haka, ko yau da safe (Litinin da ta gabata) da nake magana da kai wani abu ya taso a tsakanin malamai a Sakkwato da aka hada kai.

In abu ya taso ana hada kai, ban yanke kauna da hada kan malamai ba, in abu ya taso.

Ni nan duk matasan malaman nan suna girmama ni, misali in na kira Izalar Jos ko bangaren Kaduna za su zo duk inda nake so, sun yarda cewa tafiyar nan mun riga su cikinta suna girmama ni.

Haka gefen malaman cikin gari duk wanda na nema zan gan shi akwai mutunci tsakanina da su.

Har Malam Musa Ayuba Lukuwa da Bello Yabo, gaskiya malamai ba su da wannan tarwatsewar a Jihar Sakkwato.

Akwai alaka mai kyau a tsakaninmu, har da wadanda ban zayyano maka ba a nan, muna da hadin kai.

Daga lokacin Gwamnan Sakkwato Shehu Kangiwa zuwa yanzu yaya zamanka yake da ’yan siyasa?

Wancan lokacin ban sanya kaina a cikin hayaniyar siyasa ba, kawai in na ga sun yi abin da ba daidai ba, ko an cuci talaka zan yi bayani.

Tafiya ta yi tsawo lalura ta taso ta dole sai mun sanya hannu a harkar siyasa.

A siyasar 2015 an ga yadda ka shafa wa hotunan Goodluck Jonathan bakin fenti siyasa ce ka yi a lokacin?

Tabbas siyasa ce, an yi min tambaya kan haka na ce kiyayyarmu da Jonathan ba magana ce ta addini ko kabila ko yanki ba.

Ai Obasanjo ya yi mulki ba mu yi masa haka ba, Jonathan shi ya ja wa kansa haka ya yi alkawari ya saba, yana shafa mana kashin kaji, su ne suka sanya ba wai don yana Kirista ko wata jam’iyya ba .

Wannan shafa fentin da na yi ban saba wa doka ba, don sanya fosta a kan shataletale saba wa doka ce, bayan ba a biya kudin haraji ga jiha ko karamar hukuma ba, kuma ina son a san a Jihar Sakkwato akwai wadanda ba su yarda da takarar Jonathan ba.

Sheikh Abubakar Jibril

Hakan ya sa na tafi da ’ya’yana muka shafa masa fenti, na gaya masu wannan abin da za mu yi matukar ba a kama mu ba, to ba mu yi nasara ba.

Abin da muke so a kama mu don duniya ta sani a Sakkwato ana kiyayya da takarar Jonathan.

Wannan shi ne makasudin sanya bakin fenti a saman hotonsa, kuma bukata ta biya kada tarihi ya manta wannan ita ce asalin kiyayyar har zuwa yanzu.

Wace shawara za ka bai wa matasan malamai ganin tun kana matashi kake sadaukarwa?

Matasan malamai a yanzu in da matsalar take suna da sha’awar bukatu wadanda a lokacinmu ba mu da ita, kamar son hawan mota mai kyalkyali ko sanya shadda mai tsada ko auren mace ta ji da fadi, ko yin gida na alfarma.

Mu a lokacin gidan haya ko na aro muke zama, kuma ba mu jin wata damuwa.

Za a tafi wa’azi a kauye daga kai sai mai jan baki, sabanin yanzu da ake tafiya a gayya kuma jami’an tsaro su gewaye ka suna ba ka tsaro.

A yanzu wa’azi dan jin dadi ne ake yi, ba wata barazana daga mutanen gari ga mai wa’azi, abin ya canja don a wancan lokacin mu rigima ce a tsakanin sarakunan gargajiya da malaman tsibbu, kuma ba mu yarda da gwamnati ba gaba daya, ba ruwanmu da ita don ba ta shari’a da Littafin Allah.

Abin da zan fada wa matasan malamai su ji tsoron Allah a lamuransu, kada su biye wa rudin shahara.

Me kuke ganin ya haifar da rikicin Muslim Brothers har kuka jefar da tafiyar?

Lamarin a fili yake, ana tafiya tare gaba daya, MSS da sauran kungiyoyi suna tafe da akidar su Hasanul Banna da Sayid Kutub, tafiya ta yi nisa aka shigo da akidar da ba za ta karbu ba.

Duk kasar Ahlus Sunna da aka shigo da ita za a samu matsala, kamar ka tafi kasar Iran ce ka kawo wata kungiya ta Sunna, dole a yi rikici. Duk wanda ya zo zai canja akidar mutane sai ya samu rikici da baraka.

Matsalar akida ce aka samu. A lokacin da ba a shigo da akidar Shi’a ba, da ba a samu haka ba, domin har yanzu kungiyoyin a hade suke, MSS da NACOMYO da sauransu a hade suke suna aiki tare, in da matsala ta taso kawo abu mai hadari kwarai shi ne duban Sahaban Annabi (SAW) ka kafirta su.

Mujaddadi Sheikh Usman Dan Fodiyo ya ce “Shakkun kafircin mai kafirta Sahaban Annabi kafirci ne.”

In Sahaban Annabi (SAW) sun kafirta ai da ba Kur’ani da addinin, su ne suka kawo addini gare mu, su ne suka bayar da rayuwa da dukiyarsu a kan tsayuwar Kalmar Shahada.

Maganar a rufe su a tarihi ko a shafa masu bakin fenti da rana- tsaka tana da wahalar gaske.

Duk da suka da zagin yana cikin littattaffan Shi’a mun karanta ba ya boyuwa, hakan ne ya haifar da matsalar tafiyar a lokacin.

Duk hayaniyar da ka gani dalili ne na shigo mana da Shi’a.

Da suna kan hanyar Sunna ba wata hayaniya da za ta taso a lokacin.

Mun ajiye tafiyar ce har abada domin magana ce ta akida. Misali sunana Abubakar mahaifina ne ya sanya min sunan, fatar alheri ga Sahabin Annabi (SAW).

Na je Iran ba sau daya ba, na ga yadda akidar Shi’a take, na karanta, su suka ba mu littafai da hannunsu muka karanta wadannda ba mu cewa karya ne.

Wata rana ranar Juma’a, Ayatollah Ardalili yana Ministan Shari’a a Iran yana hudubar Jumu’a ya fashe da kuka, ya ce “Musibar da ta faru bayan Manzon Allah (SAW) ya rasu duk sahabansa sun zama kafirai in ban da ’yan kadan, yawansu ba zai wuce uku ko hudu ko biyar ba, karshen magana dukkansu dai ba su wuce bakwai ba.”

A cikinsu kuma ba Abubakar da Umar da Usman da Abu Huraira da Ibn Mas’ud da sauran manyan sahabbai, duk suna cikin masu ridda.

Ai ko wannan musiba ba karama ba ce, Sahabban Annabi (SAW) in dai ba a gode masu ba, to sun ko wuce zagi da suka da kazafi. Haka kuma ba a bar Matan Annabi (SAW) ba, musamman Uwar Muminai A’isha (RA) ita suka fi sanyawa a gaba.

Tafiya ta yi tsawo littafansu suna shigo mana muna karantawa wadansu ba su son ana fadi, har abin da ba ya faduwa a cikin jama’a mai muni mun gani a litttafansu.

Wannan ba akida ba ce mai kyau duk mai son rahamar Allah, ba zai rungumi zagin sahabbai ba, shi ne silar tarwatsewar tafiyar ‘Muslim Brothers.