✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Turawan Mulkin Mallaka ne tushen matsalar da muke ciki – Ganduje

Ya ce sun aza harsashin ginin kasar ne a kan cimma son zuciyarsu ba don ci gabanta ba

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya zargi Turawan Mulkin Mallaka da cewa su ne ummul-aba’isun matsalolin da Najeriya take fama da su a yanzu.

Gwamnan, wanda ya bayyana haka yayin bikin kaddamar da wani hamshakin dakin lakca na Naira miliyan 250 a Jami’ar Ibadan ranar Asabar, ya ce Turawan sun aza harsashin ginin kasar ne a kan cimma son zuciyarsu ba don ci gabanta ba.

A cewarsa, “Kalubalen ci gaban da Najeriya ke fama da su a yau na da nasaba da harsashin gininta zamanin Turawan Mulkin Mallaka.

“Sun yi hakan ne don kawai biyan bukatar don zuciyarsu, ba don ci gaban Najeriya na hakika ba,” inji shi.

Ya yi zargin cewa Turawan sun raba Najeriya zuwa Kudu da Arewa, ba tare da la’akari da banbance-banbancen yankunan ba.

Ya ce banbance-banbancen sun hada da na tsarin amfani da kasa, tsarin shugabanci a yankunan, ilimi da kuma tsarin shari’a ba.

Ya kuma ce kalubalen gina kasa kamata ya yi ya zama a zukatan dukkan ’yan kasar, yana mai cewa akwai bukatar sake yin duba na tsanaki a kan turbar da ake kai don barin abin koyi a nan gaba.

“Tun tsawon lokaci, bangaranci ya kasance babbar matsalar da ke ci wa Najeriya tuwo a kwarya. Shi ya sa ma ake yawan fuskantar matsaloli,” inji Gwamnan na Kano.