✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Turkiyya ta ba wa kasashen Afirka kyautar rigakafin COVID-19 15m

Gwamantin Kasar Turkiyya ta ba wa kasasnhe Afikra kyautar allurar rigakacin cutar COVID-19 guda miliyan 15. Shugaban Kasar Taurkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya shaida wa…

Gwamantin Kasar Turkiyya ta ba wa kasasnhe Afikra kyautar allurar rigakacin cutar COVID-19 guda miliyan 15.

Shugaban Kasar Taurkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya shaida wa taron hadin gwiwar Turkiyya da kasashen Afirka da aka gudanar a Birnin Santanbul cewa kasarsa za ta aiko wa kasashen da alluran wadanda karancinsu ke barazana ga al’umma.

“Muna sane da rashin adalcin da duniya ke yi wa kasashen Afirka wurin samar musu da allurar rigakafin COVID-19.

“Abin kunya ne a ce har yanzu kashi 6 cikin 100 na mutuanen kasashen Afirka ne aka yi musu allurar rigakafin,” inji shi.

Ya shaida wa taron cewa, “Muna shirin tura alluran rigakafi miliyan 15 na gaba a matsayin gudummawarmu ga kasashen Afirka.”

A halin yanzu kasar Turkiyya na kokarin samar da nata rigakafin cutar mai suna Turkovac, wanda ke gab da samun sahalewar hukumomin lafiya.

Erdogan ya ce da zararn an kammala komai, za a ba wa Afirka.

Turkiyya na bin hanyoi domin bunkasa kawancen kasuwanci da diflomasiyya tsakaninta da kasashen Afirka tun shekarar 2003.

Kwao yanzu dai babu tabbacin rigakafin da kasar ke samarwa ne za ta ba wa kasashen Afirka, ko wanda take amfani da shi na Pfizer-BioNTech ne.