✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Twitter ya amince da duk sharudan da aka gindaya —Gwamnatin Tarayya

Tattaunawa ta yi nisa kuma kamfanin ya aminta da duk sharudan da aka gindaya.

Gwamnatin Tarayya ta ce Kamfanin Sada Zumunta na Twitter, ya amince da dukkan sharudan da ta gindaya masa na ci gaba da gudanar da ayyukansa a kasar.

Hakan na kunshe cikin jawabin da Karamin Ministan Kwadago da Samar da Ayyukan Yi a Najeriya, Festus Keyamo (SAN) ya yi a wata hira da Gidan Talabijin na Channels.

Mista Keyamo wanda daya ne daga cikin mambobin kwamitin da Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa domin tattaunawa da Twitter, ya ce a halin yanzu tattaunawa ta yi nisa kuma tuni kamfanin ya aminta da duk sharudan da aka gindaya.

A cewar Keyamo, Shugaba Buhari ya dauki wannan mataki ne domin daidaita dangartakar da ke tsakanin gwamnatin Najeriya da kuma Kamfanin na Twitter ba da wata manufa ta neman korarsu ba.

Ana iya tuna cewa, a ranar 5 ga watan Yunin bana ne Gwamnatin Najeriya ta haramta amfani da shafin Twitter bisa hujjar cewa ana amfani da kafar wajen yunkurin wargaza kasar.

Sanarwar dakatar da Twitter ta zo ne jima kadan bayan da kafar ta goge wani sako da Shugaba Buhari ya wallafa wanda yake barazanar tunkarar masu fafutukar ballewa “da irin yaren da suka fi fahimta. ”

Sai dai a cikin jawabansa na cikar shekaru 61 da samun ’yancin kan Najeriya, shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa na ci gaba da gudanar da cikakkiyar tattaunawa da kamfanin na Twitter inda kuma an cimma matsaya da yarjejeniya.

A yayin da ya ce ana nan ana magance matsalolin da aka bijiro da su a lokacin tattaunawar, Shugaba Buhari ya ce ya bayar da umarnin janye haramcin da aka yi kan amfani da kafar a kasar, idan har aka cimma sharudan da aka gindaya.

Sharudan da aka gindaya sun hada da ba da damar yin amfani da shafin na Twitter ta kyakkyawar manufa, da kuma sharadin yin rijistar kamfanin a kasar.

Haka kuma an umarci kamfanin da ya rika biyan haraji, tare kuma da tsare wasu sharuda da suka danganci tsaron kasa, da kuma sanya ido a kan sakonnin da ake wallafawa.