✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Twitter ya nemi sulhu da gwamnatin Najeriya

Kamfanin Twitter ya ce a shirye yake da ya sasanta da gwamnatin, inji Minista.

Kamfanin sada zumunta na Twitter ya ce a shirye yake ya sasanta da gwamnatin Najeriya da ta dakatar da aikacen-aikacensa a kasar.

Ministan Yada Labarai da Raya Al’adu, Lai Mohammed, ya bayyana wa manema labarai cewa kamfanin ya tuntubi gwamnatin yana neman tattaunawa tare da warware kiki-kakar.

A safiyar ranar Laraba Ministan ya samu sakon tayin na kamfanin, kamar yadda ya bayyana a Fadar Shugaban Kasa bayan taron mako-mako na Majalisar Zartarwa ta Tarayya.

Lai Mohammed ya ce an dakatar da Twitter ne saboda yadda yake bayar da dama ga wadanda ke barazana ga wanzuwar Najeriya a matsayin kasa dunkulalliya.

A cewarsa, mai kamfanin Twitter ya taimaka wajen tara kudi yayin zanga-zangar #EndSARS sannan yana barin jagoran haramtacciyar kungiyar neman kafa kasar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, yana amfani da kafar wajen yin kira da a kashe jami’an ’yan sanda.

Ya ce Twitter ya kuma ya ki goge sakonnin da Nnamdi Kanun ya wallafa duk kuwa da kiraye-kirayen da aka yi wa kamfanin cewa ya goge su.

Ministan ya zayyana sharuddan da lallai sai an cika su in har gwamnatin za ta tattauna da kamfanin ciki har da dole ne kamfanin ya yi rajista a Najeriya kamar sauran masu kasuwanci a kasar.

Kazalika dole ne sauran kafofin sadar da zumunta kamar Facebook da Instagram su ma su yi rajistar aiki a cikin kasar.

Ya ce dakatar da Twitter bai kawo tarnaki ga ’yancin fadin albarkacin baki ba saboda a cewarsa ’yan Najeriya za su ci gaba da amfani da sauran kafofin sadar da zumuntar irin su Facebook da Instagram.

A karshe ya yi watsi da masu cewa dakatar da kafar da gwamnatin Najeriya ta yi bai yi wani tasiri ba, inda ya ce idan haka ne, me ya sa kamfanin tafka asarar kudade bayan matakin da Najeriya ta dauka.