✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

UAE na neman ’yan Najeriya 6 kan zargin ta’addanci

’Yan Najeriyan cikin sabbin mutum 38 da kamfanoni 15 da ake zargi da ta'addanci.

Hukumomin Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) sun bayyana sunayen wasu ’yan Najeriya shida da suke nema ruwa a jallo kan zargin ta’addanci.

Sunayen ’yan Najeriyar na cikin jerin sabbin mutum 38 da kamfanoni 15 da hukumomin Hadaddiyar Daular Larabawa suka sanya a cikin jerin sunayen ’yan ta’adda.

“Hakan na daga cikin kokarin UAE na ruguza cibiyoyin sadarwa da ke da alaka da kudaden ta’addanci,” a cewar kafar yada labarai ta Al-Arabaiya.

Wannan matakin ya zo ne kusan shekara guda bayan an gurfanar da wasu ’yan Najeriya kan zargin tallafa wa kungiyar Boko Haram, wadda ta kashe fararen hula da jami’an tsaro sama da 100,000 baya ga wasu dubban daruruwa da ta raba da muhallansu.

– ’Yan kasashen da UAE ke nema

Jerin mutum 38 din da Daular Larabawar ta fitar sun hada da wasu mutum hudu ’yan asalin kasar da wasu mutum takwa ’yan kasar Yemen.

Daga su sai ’yan Najeriya shida da ’yan Syria biyar da ’yan Iran biyar.

Akwai kuma mutum biyu ’yan kasar Lebanon, da ’yan Iraki biyu da mutum dai-dai daga Jordan da Indiya da Afghanistan da Birtaniya da Rasha da kuma Saint Kitts-Navis.

– Shari’ar ’yan Boko Haram

A Najeriya, wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta Abuja ta tsayar da ranar Juma’a 17 ga Satumba, 2021 don gurfanar da wasu mutum 400 kan zargin daukar nauyin ayyukan ta’addanci a gaban Mai Shari’a Anwuli Chikere.

A watan Maris ne Fadar Shugaban Kasa ta sanar da cafke wadanda ake zargin, yawancinsu ’yan canji, wadanda ake zargin sun taimaka wajen tura kudade ga ’yan Boko Haram.

Ana kuma zargin wasu ’yan Najeriya suna tura kudaden ga kungiyar daga kasar UAE ta hanyar amfani da ’yan canji.