✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

UAE ta dage haramcin da ta sanya wa matafiya daga Najeriya

Kamfanin Emirates ne ya sanar da hakan a shafinsa na Intanet.

Bayan kusan wata biyar, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta janye haramcin da ta sanya wa matafiya daga Najeriya zuwa kasarta daga ranar Alhamis, biyar ga watan Agustan 2021.

Kamfanin sufurin jiragen sama na Emirates ne ya sanar a shafinsa na Intanet cewa daga ranar, matafiya daga Najeriya da wasu kasashe 10 da ke da sha’awar shiga kasar kuma suka cika ka’idoji za su iya yin haka.

Kasashen dai sun hada da Indiya, da Pakistan da Sri Lanka da Uganda da Vietnam da Afirka ta Kudu da Afghanistan da Indonesia da Bangladesh da kuma Nepal.

Emirates, a wani gajeren sako da ya wallafa ya ce, “Za mu wallafa cikakkun bayanan abubuwan da ake bukatar masu sha’awar tafiya su tanada a bangaren kula da matafiya na shafinmu da zarar sun kammala.”

Tun a watan Maris din wannan shekara dai aka dakatar da zirga-zirgar jirage tsakanin Najeriya da UAE sakamakon tsamin dangantaka a kan cutar COVID-19.

Yayin da Gwamnatin Tarayya ta sanya gwajin cutar a matsayin abin da ake bukata ga matafiya zuwa Dubai, ita kuwa kasar ta kara da wani gwajin a matsayin sharadi, lamarin da Najeriya ta ki amincewa da shi, har ya kai ga hana jiragen kamfanin Emirates mallakar kasar daga zuwa Najeriya.

Ko da yake daga bisani an dage haramcin, amma kamfanin bisa umarnin kasar ta UAE ya dakatar da ci gaba da zuwa Najeriya.

Aminiya ta rawaito cewa jiragen da ke tashi daga Legas zuwa Dubai da wadanda ke tashi daga Abuja zuwa Dubai na daga cikin wadanda suka fi kawo wa kamfanin kudaden shiga.

Kazalika, dillalan kamfanonin sufurin jiragen na samun matukar riba daga tikitin da suke sayarwa ga fasinjoji masu tafiya zuwa kasar.