✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Uba Sani ya samu tikitin takarar Gwamnan APC a Kaduna

Sanata Uba Sani ya lashe zaben fid da gwanin Gwamna na jam'iyyar APC a Jihar

Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya a Majalisar Dattijai, Uba Sani, ya samu nasarar lashe zaben fid da gwanin Gwamna na jam’iyyar APC a Jihar Kaduna.

Uba Sani, wanda shi ne dan takarar Gwamna Nasir El-Rufa’i, ya samu kuri’a 1,149 wanda hakan ya ba shi damar doke tsohon Mataimakin Shugaban Hukumar Kwastam, Bashir Abubakar da kuma tsohon dan Majalisar Wakilai, Alhaji Mohammed Sani Sha’aban.

Aminiya ta ruwaito cewa zaben fid da gwanin da aka kammala a dakin taro na Umaru Yar’adua da ke dandalin Murtala Square da misalin karfe 2:15 na safe ya samu kuri’u 39 wanda ba su inganta ba.

Da ya ke bayyana sakamakon zaben, shugaban kwamitin zaben na jam’iyyar APC, Anachuna Henry, ya bayyana Uba Sani a matsayin wanda ya lashe zaben, inda ya ce jam’iyyar na da wakilai 1,275 amma 1,245 ne aka amince da su kada kuri’a, yayin da kuma mutum 1,196 daga cikinsu ne suka kada kuri’unsu.

A nasa jawabin, Sanata Uba Sani, ya yaba wa wakilai da jami’an jam’iyyar da kuma alkalan zaben.

Kazalika, ya kuma ba da tabbacin zai kai ziyara ga ragowar masu neman takarar biyu da ba su yi nasara ba, domin su yi aiki tare don kai jam’iyyar ga gaci.