✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Uba ya guntule wa dansa hannu saboda kungiyar asiri

Wani mutum ya yanke wa dansa haddi saboda zargin ayyukan kungiyar asiri a garin Nyangansang da ke Kalaba, Jihar Kuros Riba. Mutumin ya fille wa…

Wani mutum ya yanke wa dansa haddi saboda zargin ayyukan kungiyar asiri a garin Nyangansang da ke Kalaba, Jihar Kuros Riba.

Mutumin ya fille wa dansa hannu ne sakamakon sa-in-sa tsakaninsu bayan an kawo masa kara cewa yaron dan kungiyar asiri ne.

Dan uwan mutumin ya ce karar yaron da aka kai wa mahaifinsa cewa ya shiga kungiyar asiri da sauran laifuka ta sa ya yi masa haddi.

Ya kuma shaida wa wakilinmu cewa mutanen garin na cikin fargaba saboda alwashin daukar fansa da ‘yan kungiyar asiri suka sha.

Shugaban matasan garin, Timothy Sam, ya ce ‘yan sanda sun sha kama yaron kan mu’amalolinsa da yake aikatawa cikin dare.

“Da sanyin safiyar Lahadi, aka ce ya yi kokarin sassara mahaifin nasa saboda ya ki ba shi goyon baya.

“Mahaifin ya fille masa hannu ne a yunkurinsa na kare kansa”, inji majiyar.

Kokarin da Aminiya ta yi na ji daga bakin mutumin da dansa ta ci tura.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na Jihar Kuros Riba, Irene Ugbo ta ce ba ta da labarin aukuwar lamarin, amma za ta gudanar da binciken.