✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Uba ya yi wa ’yar cikinsa fyade a Legas

Wata Kotun Majistare a Ikejan jihar Legas ta sa a tsare wani mutum mai shekara 40 da kuma abokinsa a gidan gyaran hali na Kirkiri…

Wata Kotun Majistare a Ikejan jihar Legas ta sa a tsare wani mutum mai shekara 40 da kuma abokinsa a gidan gyaran hali na Kirkiri a bisa zargin yin lalata da ’yar cikinsa mai shekara tara da haihuwa.

Rundunar ’Yan Sanda ta jihar na tuhumar mutumin mai suna Udoh, shi makwabcinsa Chi Abellaga da cin zarafina karamar yarinyar da kuma keta mata haddi.

A cewar mai gabatar da kara na rundunar ’yan sandan jihar ASP Raji Akeem, wadanda a ke zargi sun aikata laifin ne a tsakanin watannin Afrilu da Yuli na shekarar 2022.

Mai unguwar da suke zaune ne ya kawowa ’yan sanda karar Mista Udoh da Abellega a ofishinsu, inji Akeem.

Ya kuma ce, yarinyar mai shekara tara ta tabbatar wa da ’yan sanda cewa mahaifin nata da abokinsa sun ci zarafinta.

Alkalin Kotun Mrs B.O Osunsanmi ta ki karbar hanzarin wandanda ake tuhuma da cewa ba ta da hurumin yi musu shari’a.

Mai Sharia’a ta ummarci jama’in ‘yansanda da su mika takardun karar ga Babbban Mai Gabatar da kara na jiha domin shawarwari.

Sannan Alkalin ta dage sauraron karar zuwa ranar 24 ga watan Agusta, ta kuma bayar da umarnin da a cigaba da tsare wadanda ake zargi a gidan maza na Kirikiri.