✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

UEFA: Atletico Madrid da Man-U sun tashi 1-1, Benfica da Ajax 2-2

Duka wasannin biyu an tashi kowace kungiya na nema.

Manchester United ta rike Atletico Madrid har gida inda aka tashi kowa na da kwallo daya a ragarsa, yayin da Benfica da Ajax suka tashi 2-2.

A daren ranar Laraba ne a ci gaba da gasar gasar Zakarun Turai, inda Atletico Madrid ta karbi bakuncin Manchester United, Benfica kuma ta karbi bakuncin Ajax.

An buga wasan Atletico Madrid da Manchester United ne a filin wasa na Wanda Metropolitano da ke birnin Madrid a kasar  Spain.

Dan wasan gaban Atletico Madrid, Joao Felix ne ya fara zuwa kwallo a minti na bakwai da fara wasa, sai kuma dan wasan Manchester United Anthony Elanga ya warware kwallon a minti na 80.

A karawar Benfica da Ajax kuwa leda aka murza mai ban sha’awa a filin wasa na Estadio da Luz da ke kasar Portugal.

Dan wasan Ajax Tadic ne ya fara cin kwallo a minti na 18, daga baya kuma Haller, wato dan wasan gaban Ajax ya zura kwallo a ragar kungiyarsa (own goal) a minti na 26.

A minti na 29 Haller ya kara kwallo ta biyu a ragar Benfica, sai kuma Yaremchuk ya zare kwallon a minti na 72.

Haka aka tashi duka wasannin biyu, wato kowa na nema; Za a dawo zagaye na biyu na wasan a ranar 15 ga watan Maris, 2022.