✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

UEFA ta hukunta Ingila kan rashin da’a a gasar EURO2020

UEFA ta kuma ci tarar tawagar Three Lions fam 84,560.

Hukumar Shirya Kwallon Kafa ta Turai wato UEFA, ta haramta wa Ingila damar bai wa magoya baya shiga kallon wasanta na akalla wasa guda cikin shekarar nan.

UEFA ta kuma ci tarar tawagar Three Lions fam 84,560 a matsayin hukuncin nuna rashin da’a da magoya bayanta suka nuna a wasan karshe na gasar EURO2020 da aka yi a filin wasa na Wembley.

Wannan hukunci na zaman ladabtarwa kan kamen da ya biyo bayan wasan karshe na gasar EURO2020 a filin wasa na Wembley da ke London.

Bayanai sun ce a lokacin ’yan sandan Birtaniya suka sanar da kama mutun 51.

A cewar UEFA, magoya bayan na Ingila sun tayar da tarzoma bayan rashin nasarar kasar hannun Italiya a bugun daga kai sai mai tsaron raga wato fenariti.

Yayin hukuncin dai wasanni biyu UEFA ta zartaswa Ingilar ta yi ba tare da ’yan kallo ba, amma ta dage wasa guda har sai nan da shekaru 2 masu zuwa.

UEFA ta ce ta kadu matuka bayan ganin abin da ya faru a filin wasan na Wembley cikin watan Yuli yayin wasan na karshe.

Shugaban Hukumar Aleksender Ceferin ya ce abin takaici ne ganin cewa wasu daga cikin wadanda suka haddasa tarzomar har yanzu suna da sukunin iya shiga kallo a filayen wasanni.

’Yan kallo sun rika fada da masu kula da filin Wembley da kuma yan sanda, a kokarinsu na shiga filin wasan ta karfi a ranar 11 ga watan Yuli, inda Ingila ta yi rashin nasara a hannun Italiya.

Lamarin ya sa wasu ’yan kallo sun jikkata, ciki har da mahaifin kyaftin din Ingila kuma mai tsaron bayan Manchester United, Harry Maguire.

Sai dai a martanin da ta yi, Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila ta nuna rashin jin dadinta da hukuncin na UEFA, amma kuma duk da haka ta ce ta yi na’am da shi.