✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ukraine ta sanya dokar hana fita a birnin Kyiv

Dokar za ta fara aiki daga karfe 8 na daren ranar Litinin

Gwamnatin Ukraine ta ayyana dokar hana fita na tsawon kwana uku a birnin Kyiv, fadar gwamnatin kasar.

Magajin Garin Kyiv, Vitali Klitschko, shi ne ya sanar da dokar ta shafinsa na Telegram a safiyar Litinin, ya kuma bayyana cewa dokar za ta fara aiki ne daga karfe 8 na dare.

“Dokar hana fitar za ta fara aiki ne daga karfe 8 na dare ranar Litinin har zuwa karfe 7 na safe (karfe 5 na asuba agogon GMT) ranar 23 ga Maris, 2022” inji sakon da  Klitschko ya fitar ta Telegram.

An kafa dokar ce sa’o’i kadan bayan wani kazamin hari da Rasha ta kai a cikin dare kan wani katafashen shagon kasuwanci na Retroville a Kyiv, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum shida a safiyar Litinin.

Jami’an tsaro da ’yan kwana-kwana na ci gaba da aikin ceto taer da bincike a cikin baraguzan benen mai hawa 10 domin hako mutanen da ginin ya rufta a kansu.

Shaidu sun ce karfin abin fashewar da ya fada wa ginin ya girgiza birnin Kyiv, tare da yi watsi da motoci tare da lalata sauran abubuwan da ke wurin.

Sojoji sun killace wurin tare da gargadin cewa akwai yiwuwar fashewar ragowar makaman da aka harba wa ginin ba su riga sun fashe ba.

Gilasan tagogin makwabtan wurin duk sun farfeshe, inda mutane ke cewa an yi kwana suna ganin makaman harba rokoki a kusa da shagon kasuwancin.

An yi kwanaki Kyiv na fama da hare-haren Rasha, ciki har da wani da ya fadi a kan wani gida inda ya jikkata mutum biyar.

Duk da haka dai, yunkurin Rasha na shiga Kyiv ya fuskanci turjiya daga dakarun Ukraine, inda aka kwashe kusan mako biyu anamusayar wuta a yankin Gabas da kuma Arewa maso Yamma.