✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ukraine ta yi ikirarin hallaka dakarun Rasha 4,300

Sai dai ba a kai ga tantance gaskiyar alkaluman ba tukunna.

A ci gaba da gwabzawar da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine, kasar ta Ukraine ta yi ikirarin hallaka dakarun Rasha 4,300 tun bayan fara yakin.

Mataimakin Ministan Tsaron Ukraine, Hanna Malyar, ne ya fitar da alkaluman a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Sai dai babu wasu bayanai da za su tabbatar da gaskiyar ikirarin na Ukraine kan adadin ko kuma akasin haka.

Mista Hanna Malyar ya ce sun tabbatar da adadin, inda ya kuma ya yi ikirarin cewa dakarun kasarsa sun kuma lalata tankokin yaki 146 da jiragen yaki guda 27 da kuma jirage masu saukar angulu guda 26, dukkansu mallakar Rasha.

Sai dai har zuwa yanzu kasar ta Rasha ba ta mayar da martani ba kan ikirarin na Ukraine.

Bugu da kari, Ukraine ta kuma kakkabo wani makami mai linzami kirar Tu-22 da Rashar ta harba musu.

Babban Kwamnandan sojojin Ukraine, Valery Zaluzhny, ne ya tabbatar da harbor jirgin, wanda ya ce sun kakkabo shi ne daga kasar Belarus mai makwabtaka da su.