✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ukraine za ta rage yawan ma’aikatunta, ta kuma sallami ma’aikata

Gwamnatin Ukraine na shirin rage yawan ma’aikatun kasar daga 20 zuwa 14, da kuma sallamar wasu daga cikin ma’aikatanta. Wannan matakin ya biyo bayan taron…

Gwamnatin Ukraine na shirin rage yawan ma’aikatun kasar daga 20 zuwa 14, da kuma sallamar wasu daga cikin ma’aikatanta.

Wannan matakin ya biyo bayan taron da Shugaban Kasar, Volodymyr Zelensky, da sauran masu fada a jin kasar suka gudanar kan kawo sauyi a bangaren gudanar da ayyukan gwamnati.

Yanzu haka dai wata kafar yada labaran kasar ta rawaito cewa za a hade Ma’aikatar Kula da Tattalin Arzikin kasar da ta Kula da Masana’antu, sai kuma Ma’aikatar Noma da za a hade ta da ta habaka Tattalin arziki da za a kirkira.

Kazalika, Ma’aikatar Fasaha za ta hade da ta kula da walwalar ma’aikata, da wani sashe na ma`aikatar tsare-tsaren kamfanoni.

Sai dai wannan canjin dai ba zai shafi Ma’aikatar Hulda da Kasashen Waje ba, da ta Tsaro, da ta Kudi, da ta Lafiya, hadi da Ilimi.

Rahoton ya kara da cewa ma’aikata kuma za a rage su daga 9,200 zuwa 2,800, sai kuma ma’aikatun da ke aiki a ofisoshin yanki daga 17,000 zuwa kusan 7,000.