✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ummita: Rashin shaida ya kawo tsaiko a Shari’ar dan China

An kasa ci gaba da Shari'ar kisan Ummukulsum Buhari (Ummita), matashiyar da ake zargin saurayinta dan kasar China ya kashe ta a Kano.

An kasa ci gaba da Shari’ar kisan Ummukulsum Buhari (Ummita), matashiyar da ake zargin saurayinta dan kasar China ya kashe ta a Kano.

Rashin halartar zaman kotu da shaidar masu gabatar da kara ya yi ranar Litinin ya kawo tsaiko a shari’ar da ake yi tsakanin Gwamantin Jihar Kano da dan Chinan, Mista Frank Geng Quarang.

Gwamnatin ta gurfanar da Mista Gungrong ne kan kashe masoyiyar tasa a gidan iyayenta da ke unguwar Janbulo a Jihar Kano a ranar 16 ga watan Satumba, 2022.

A zaman da ya gabata, masu gabatar da kara karkashin jagorancin, Kwamishina Shari’a na Jihar Kano, Barista M. A. Lawan sun gabatar da shaidu biyar da suka hada da mahaifiyar marigayiya Umimta da kanwarta da makwabcinsu da kuma ’yan sanda biyu daga Sashen Binciken Manyan Laifuka na Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano.

Sun kuma gabatar wa kotu wukar da ake zargin wanda ake tuhuma ya yi amfani da ita wajen kashe Ummita a matsayin hujja abar nuni.

Sai dai a zaman kotun na ranar Litinin, lauyan masu gabatar da kara Barista Wada A. Wada ya shaida wa kotun cewa kasancewar mahaifin wanda za su gabatar wa kotu a matsayin shaida na shida ba shi da lafiya, ba za su iya ci gaba da shari’ar ba, inda suka nemi kotu ta dage shari’ar zuwa ranar Laraba.

“Muna neman afuwa cewa ba za mu iya gabatar da shaidanmu na karshe a yau ba, saboda mahaifinsa ba shi da lafiya sosai wanda ta kai shi shaidan namu ne ke jinyar sa a asibiti, hakan ya sa muke neman a dage mana shari’ar zuwa Laraba idan Allah Ya yarda shaidarmu zai bayyana”

Lauyan wanda ake kara, Barista Muhammad Danazumi, bai yi suka game da hakan ba, inda ya nuna cewa rashin lafiya babban dalili ne da zai sa a dage shari’a.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Sanusi Ado Ma’aji ya dage shari’ar zuwa ranar 21 ga watan Disamba, 2022 don ci gaba da sauraren shaidu.