✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Uwargida ta kashe miji a daren kwanan amarya

Ana zargin ta kashe mijin ne ta hanyar daba masa wuka.

Rundunar ’Yan sandan Jihar Nasarawa tana ci gaba da gudanar da bincike a kan wata mata da ake zargi da kashe mijinta ta hanyar daba masa wuka.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:00 na dare ranar Asabar da ta gabata a Unguwar Yarima da ke garin Marararaban Guruku a Karamar Hukumar Karu da ke iyaka da Abuja.

Wata majiya a gidan ta shaida wa Aminiya cewa, wadda ake zargin mai suna Atika mai ’ya’ya 3 da marigayin mai suna Ibrahim Salihu mai shekara 37 da ke sana’ar kanikanci, ya je dakinta a daren don yi mata bankwana don wucewa dakin amarya inda takaddama ta shiga tsakaninusu.

“Yakan yi kwana biyu a dakin kowace, sannan dabi’arsa ce yin sallama da wadda zai fita daga dakinta kafin ya koma dakin dayar.

“Kuma haka ta kasance a ranar sai dai ana cikin haka sai ta cije shi a yatsa.”

Mahaifiyar marigayin, Hajiya Hauwa Umar da ta je gidan bayan babban dan matar ya sanar da ita ta waya abin da ya faru da mahaifinsu, ta shaida wa Aminiya cewa bayanin da ta samu shi ne amaryar marigayin ta yi yunkurin ba shi agajin gaggawa ta hanyar daure masa yatsar da uwargidan ta ciza, sai dai ana cikin haka, sai uwargidan ta sake damkarsa ta baya, sannan ta daba masa wuka a wuya da ciki.

Ta ce uwargidan wadda ta yi hakan bayan rufe kofar gidan, ta bi mijin nata da gora a lokacin da ya yi yunkurin gudu waje, lamarin da ya kai shi ga faduwa kasa, rai ya yi halinsa.

Aminiya ta samu labarin cewa wani abin mamaki da ya sake aukuwa a lokacin da ake yunkurin kai marigayin asibiti, shi ne yadda wadda ake zargin ta rika ihu tana rungumar mijin tare da bukatar a taimaka mata cewa ta kashe mijinta.

Wata majiya ta ce “Har ta yi yunkurin zama a babur din da aka dora shi a kai, amma sai aka ture ta gefe guda aka kai shi asibitin, inda a ka tabbatar ya rasu.”

Aminiya ba ta samu jin ta bakin wadda ake zargin ba, sai dai wadansu makusantanta sun ce, ta jima tana korafi tare da zargin nuna fifiko ga amaryar daga bangaren mijin.

“Ta ce ko taliyar Indomi ce ya sayo, sai ya ba wa kowacensu kwali daya duk da cewa uwargidan ’ya’yanta uku ne, ita kuma amarya a yanzu ne ta samu ciki.

“Ko a daren da lamarin ya faru, amaryar ta fada wa mijin cewa tana son cin kifi, sai suka fita tare ya saya mata su ka dawo gida,” inji majiyar.

Yunkurin jin ta bakin wani dan uwan marigayin ta waya mai suna Alhaji Sani Zangina, wanda shi ne Shugaban Kungiyar Masu Harkar Fuloti a Karamar Hukumar Karu bai samu nasara ba.

An yi jana’izar marigayin a safiyar Lahadin da ta gabata kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.