Uwargidan shugaban Amurka ta ziyarci Ukraine | Aminiya

Uwargidan shugaban Amurka ta ziyarci Ukraine

Jill Biden tare da Olena Zelenska a Ukraine
Jill Biden tare da Olena Zelenska a Ukraine
    Ishaq Isma’il Musa

Uwargidan Shugaban Amurka, Jill Biden ta kai ziyarar ba-zata a Ukraine yayin balaguron da take yi zuwa Romania da Slovakia, inda ta jaddada goyon bayan Amurka ga kawayenta na NATO.

Mrs Biden ta gana da matar shugaban Ukraine Olena Zelenska a wata makaranta da ke garin Uzhhorod, wanda yanzu ake amfani da ita a matsayin wurin buya ga fararen hula.

Uwar gidan Biden din ta ce ta so ne ta nuna cewa “Amurkawa na tare da jama’ar Ukraine”, inda ta kara da cewa yakin wanda yanzu ya shiga wata na uku “na rashin imani ne” kuma dole a dakatar da shi.

BBC ya ruwaito matar shugaban Ukraine tana cewa abu ne “na bajinta” mutum ya ziyarci kasar a irin wannan lokaci.

“Mun fahimci irin hadarin da mai dakin Biden ta saka kanta a ziyarar da ta kawo Ukraine, lokacin da ake ta barin wuta a kowace rana, ake kunna jiniya kowace rana, har a yau,” in ji ta.