✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Varane zai yi jinyar wata daya

Varane ba zai buga wasannin da United za ta kara da City da kuma Chelsea ba.

Mai tsaron bayan Manchester United Raphael Varane zai shafe kusan wata daya yana jinya.

Wannan dai ta kasance ne bayan Varane din ya samu rauni a wasan Zakarun Turai da United ta tashi 2-2 da Atalanta ta Italiya a ranar Talata.

A watan Agusta ne dan Faransan mai shekaru 28 ya tafi United daga Real Madrid kan fam miliyan 34 kuma bai jima da dawowa daga wani raunin ba.

Jinyar da Varane zai yi na nufin ba zai buga wasannin Premier League da kulob dinsa zai yi da Manchester City da kuma Chelsea ba.

Shi ma mai tsaron baya Victor Lindelof bai samu tafiya Italiya wasan Atalanta ba saboda rauni, gashi kuma tauraruwar kyaftin din kungiyar Harry Maguire ta fara dusashewa.