✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Victor Moses zai yi wata 6 bai buga kwallo ba

Kungiyar Spartak wacce Victor Moses ke buga wa kwallo ita ce mafi tashe a Rasha.

Tsohon dan wasan tawagar Super Eagles ta Najeriya, Victor Mosses, zai shafe watanni shida ko fiye ba tare da ya taka leda ba.

Victor Moses wanda a yanzu yake murza leda a kungiyar Spartak Moscow da ke Rasha, zai shafe watanni shidan ne ba tare da buga kwallo ba a sakamakon wani rauni da ya samu.

Rahotanni sun tabbatar da cewa za a yi wa dan wasan tiyata sakamakon raunin da ya samu a kafa yayin wasan gasar Firimiyar Rasha da kungiyarsa ta buga ranar Asabar.

A minti na 33 ne dai Mikhail Ignatov ya canji Moses a fafatawar da Spartak Moscow ta doke kungiyar Ural da ci 2-0 a filin wasa na Ekaterinburg Arena.

Lokacin da aka cire Victor Moses bayan ya ji rauni.

Kungiyar Spartak wacce Victor Moses ke buga wa kwallo na daya daga cikin kungiyoyi da ke tashe a kasar Rasha.

Kafin kowawarsa Spartak a 2018, Moses ya taka leda a kungiyar Chelsea da ke Landan, inda ya ci mata kwallaye 18 a wasanni 128 da ta kai su ga lashe gasar Europa.

Kafin nan,  Victor Moses ya ci kwallaye 12 a wasannin 27 da ya buga a yankin Afirka ta Yamma.

Ya taka rawa a nasarar da Najeriya ta samu wajen lashe kofin nahiyar Afirka (CAF) a 2013.

Tsohon dan wasan na kungiyoyin Crystal Palace, Wigan, Liverpool, West Ham, Inter Milan da kuma Fenerbahce, ya wakilci Najeria a gasar Cin Kofin Duniya karo biyu a shekarar 2014 da kuma 2018.