✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Wa ke da gaskiya tsakanin kafafen yada labarai da Muhammad Garba?

Shin tsakanin kafafen yada labarai da Mal. Muhammad Garba, wa za a gaskata?

Sunan tsohon shugaban Kungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) kuma tsohon Shugaban ’Yan Jarida ta nahiyar Afirka kuma Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba ba bako ba ne musamman ganin irin kwarewar da ya samu a harkar aikin jarida a ciki da wajen Jihar Kano.

Tarihin wannan gogaggen dan jarida ya nuna cewa ya fara aikin jarida ne tun daga 1989 a kamfanin buga jaridu na ‘Triumph’, mallakin Gwamnatin Jihar Kano.

A cikin irin aikace-aikacensa na yada labarai ya taba zama sakataren yada labarai na Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilan Najeriya a 1993.

Amma duk da tarinsa ilimi da kwarewa da sanin aiki da Malam Muhammad Garba yake da su, sai ga shi a farkon makon nan da mu ke ciki al’ummar Najeriya suka cika da al’ajabin yadda ya yi wani abu da za a ce na kunya ne ko kuma makuwa ce a aikin jarida.

Domin idan da a kasashen da suka ci gaba ne babu shakka da tuni Garba ya dade da sauka daga mukaminsa saboda wannan abin kunya da ya aikata.

Duk da cewa masana da masu sharhi a kan al’amuran yau da kullum sun dade suna batun cewa duk dan jaridar da ya karbi aiki a gurin gwamnati irin ta siyasa, to tabbas ya zama dan amshin shata, ma’ana sai abin da mahukunta suke so zai fada a kan kowacce irin mas’ala kuma ko da hakan zai zubar masa da martaba da darajar aikin da ya yi shekara  da shekaru yana nema wa kansa.

Amma kuma a daya bangaren, kowa yana sane da cewa tsira da martaba da mutunci ya fi duk wani abu da bawa zai samu a wannan sararin duniyar.

Haka kuma ga mutane irin su Muhammad Garba da suka shafe fiye da shekara 30 suna fafatukar gina rayuwar aikinsu a kan daraja da martaba da kuma kima, abun mamaki ne kwarai da gaske a ce rana tsaka su barar da wannan gini na tsawon shekaru.

Mene ne ya faru?

A ranar Litinin 5 ga watan Oktoba, 2021, jaridar Premium Times da ke shafukan intanet ta rawaito cewa hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta kama Hajiya Hafsat Abdullahi Umar Ganduje, uwar gidan Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, kan tuhumar rashawa da zambar fili da danta ya kai karar ta.

Baya ga jaridar ta Premium Times kafafen yada labarai irin su Daily Trust, BBC Hausa, DW, Rfi da VOA duk sun rawaito wannan labarin.

Kuma babu shakka shi kan sa Malam Muhammad Garba ya yi imani da cewa babu yadda za a yi wadannan kafafen yada labarai na gida da na waje da duniya ta aminta da sahihanci da ingancin labaransu su hadu a kan labari guda wanda kuma ba sahihi ba ne! Abu ne mai wahala.

Domin wata tabbatacciyar majiya daga fadar gwamnatin Kano da ta bukaci a sakaye sunanta, ta sanar wa sashen Hausa na BBC cewa jami’an hukumar EFCC ne suka je har Kano suka kuma tafi da Hafsat Abdullahi Umar Ganduje wadda aka gayyata zuwa ofishin hukumar da ke Abuja, domin amsa tambayoyi masu nasaba da korafin da danta ya gabatar wa hukumar.

Sai dai jim kadan da bullar wannan labari sai ga shi Malam Muhammad Garba ya fitar da wata sanarwar da ke ikirarin cewa wannan labari karya ne, ma’ana ba shi da tushe balle makama! Kaico!

Amma a wani al’amari mai kama da tufka da warwara tare da rashin kwarewar wasu daga cikin masu taimaka wa gwamnatin Kano a kan harkar yada labarai, sai ga shi daya daga cikin masu taimaka wa Gwamna Ganduje kan yada labarai ya wallafa wasu hotuna a shafukan sada zumunta na Facebook da ke nuna Hajiya Hafsat Abdullahi Umar Ganduje tana sauka daga jirgin sama a filin tashi da sauka na Malam Aminu Kano da ke birnin Kano.

Wannan jami’i ya kara wa hoton da wani gajeren rubutu kamar haka “Mai girma gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, tare da mai dakinsa Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje sun sauka a filin sauka da tashin jirage na Malam Aminu Kano bayan dawowa daga Birnin Tarayya Abuja a safiyar wannan rana. Yau, Talata 5/10/2021”

Abin lura a nan shi ne ko iya wannan kadai ya isa a ce Malam Muhammad Garba ya ki amincewa ya fitar da sanarwar da ke nuna cewa labarin gayyatar da hukumar EFCC ta yi wa uwar gidan gwamnan Kano karya ne.

Domin hotunan sun jefa kokwanto tare da shakku kan al’amuran biyu, wato batun kwamishinan cewa “Goggon” ba ta je Abuja ba da kuma hotunan da ke nuna dawowarta Kano daga Abuja.

Kazalika, idan har irin wadancan kafafen yada labarai za su rawaito labarin da suke da ingantacciyar madogara tare da hujjoji kwarara, amma kawai don ya saba wa wani mai mulki, sai kawai a fito a ce labarin karya ne?

To wadanne kafafen yada labarai ne ke nan za su rawaito sahihin labari?

Yanzu dai tambayar guda daya ce; shin tsakanin Premium Times, Daily Trust, BBC, DW, Rfi da VOA da kuma Malam Muhammad Garba wane ne mai gaskiya da ’yan Najeriya za su yarda da shi?

Al’umma su ne alkalai.

Buhari Abba dan jarida ne da ya rubuto daga Kano, Najeriya.

Imel: buhariabba57@gmail.com